✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude makarantu a China bayan sassauta dokar hana fita

A yayinda kasashen duniya ke kokarin dakile yaduwar cutar coronavirus, dalibai sun fara komawa makarantu a kasar Sin bayan hukumomi sun sassauta dokar hana fita.…

A yayinda kasashen duniya ke kokarin dakile yaduwar cutar coronavirus, dalibai sun fara komawa makarantu a kasar Sin bayan hukumomi sun sassauta dokar hana fita.

Dalibai a manyan biranen kasar na Shanghai da Beijing sun fara komawa azuzuwansu bayan share watanni uku a kulle a gida.

Hukumar ilimi ta kasar ta bayyana cewa za a tsaurara matakan kariya a kofofin shiga makarantun.

Hukumar ta kuma ce za a gudanar da gwaje-gwaje a kan duk wandanda za su shiga harabobin makarantun da kuma tabbatar da an kula da matakan kariya da hukumomin lafiya suka gindaya.

Wata daliba a birnin Shanghai mai suna Hang Huan ta bayyana farin cikinta da sake bude makarantun.

“Na yi farin ciki. Na dade ban hadu da abokan karatuna ba kuma na yi kewarsu sosai”, inji ta.

Cutar ta coronavirus dai ta bulla ne a garin Wuhan a kasar ta China, inda ta kashe sama da mutane dubu hudu zuwa yanzu.

Bayan kasar ta China, kasashen Norway, da Switzerland, da New Zealand, da Spaniya, da Saudi Arabia da Turkmenistan duk sun fara shirin sassauta dokar hana fitar da suka ayyana saboda dakile yaduwar cutar ta coronavirus da ta yi barna a kasashe da dama.

A gefe guda kuma, kwararru suna ganin lokaci bai yi ba da za a janye dokar hana fita saboda gudun abin da ka iya faruwa.

Dokar hana fitar dai ta sa komai ya tsaya cak a kasashe da dama.