Gwamnatin Jihar Kano ta bude makarata na musamman domin yara masu baiwa ta musamman a Jihar da ma fadin Najeriya.
Makarantar za ta dauki yara masu baiwa ta musamman biyar-biyar a kananan hukumomi Jihar 44, da kuma biyu-biyu daga sauran Jihohin Arewa 18.
- Likitoci uku sun rasa rayukansu a Kano
- Katin dan kasa: An cafke masu yin rajista na bogi a Kano
- Dole shugabannin makarantu su rika kwana a cikin dalibai — Ganduje
- Za a fara hukunta marasa amfani da takunkumi a Kano
Kwamishinan Ilimin Jihar Kano, Muhammad Sanusi Kiru ya ce watan Maris na 2021 ne daliban farko za su fara karatu a makarantar da aka kafa don ingatawa da tattala basirar da Allah Ya ba wa yaran.
“Mun yanke shawarar hada su waje daya tare da samar musu da abin da suke bukata, sannan muna da wakilai daga kowace karamar hukuma.
“Za mu ba wa jihohin Arewa gurbin dalibai biyu-biyu, na tattauna da Gwamna Ganduje kuma ya amince da hakan,” inji shi.
A cewarsa, makarantun yara masu baiwa ta musamman biyu ne kacal a Arewacin Najeriyar a Jihar Jigawa da Abuja sai kuma ta Jihar Kano a yanzu.
A watan Nuwamban 2020 ne aka kafa makarantar da ke garin Ganduje, mahaifar Gwamna Abdullahi Ganduje, a Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar.
Da yake mika fom din jarabawar shiga makarantar ga wakilan gwamnati a ofisoshin shiyyoyi, Kwamishinan ya yi musu kashedi a kan magudin jarabawa.
A shekarar da ta wuce ne Gwamnatin Kano ta sake kaddamar da ilimi kyauta a fadin jihar.