✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude iyakar Gaza don shigar da kayan agaji

Masar ta bude iyakar Zirin Gaza domin shigar daruruwar motocin kayan agaji ga Falasdinawa daga ranar Juma'a

Kasar Masar ta bude iyakarta da Zirin Gaza ta yankin Rafah domin shigar daruruwar motocin kayan agaji zuwa yankin Falasdinawa da Isra’ila ta yi wa luguden wuta na kwanaki 12.

Kakakin shugaban kasar Masar, Ahmed Fahmy ya sanar a safiyar Alhamis cewa, “Shugaba Abdel Fattah al-Sisi da takwaransa na Amurka, Joe Biden sun amince a ci gaba da shigar da kayan agaji zuwa Zirin Gaza ta iyakar Rafah.”

Tattaunawar da ta kai ga bude iyakar ta yankin Rafah ya ce ranar Juma’a motocin kayan agaji za su fara shiga Zirin Gaza, amma za a kayyade adadin motocin da za su shiga.

Tuni jirage suka fara lodin kayan jinkai da Majalisar Dinkin Duniya ta ware wa Falasdinawa zuwa Zirin Gaza daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

A ranar Alhamis Rasha ta tura wa Falasdinawan jirgi dauke da ton 27 na tallafin abinci da za a shiga yankin ta kasar Masar, domin rage radadin barnar da Isra’ila ta yi wa yankinsu.

Tun bayan barkewar sabonn rikicin Hamas da Isra’ila daruruwan motocin kayan agaji suka yi jerin gwano a iyakar Rafah, wanda kasar Masar ke iko da shi, ba tare da sun samu izinin tsallakawa ba.

Akalla mutane miliyan daya ne suka rasa muhallansu a Gaza a sakamakon ruwan bama-baman da jiragen Isra’ila suka yi wa yankin na tsawon kwanaki 13.

A makon jiya ne Isra’ila ta hana shiga da fita daga Zirin Gaza, inda sojojinta suka yi wa yankin kawanya, suka kuma yanke wutar lantarki da ruwan sha da kuma hana kai komon abubuwan bukata.

A ranar Talata Ofishin Shirin Abinci na Duniya (WFP) ya sanar cewa abincin da ya rage a Zirin Gaza ba zai wuci kwana biyar ba, a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta la’anci datse yankin da Isra’ila ta yi.

Kasashe da kungiyoyi da dama daga sassan duniya sun la’anci kisan gillar da Isra’ila ta yi wa Falasdinawa fararen hula a Gaza, da kuma yanke musu hanyoyin rayuwa da sunan yaki da kungiyar Hamas.