✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude filin jirgin sama na Malam Aminu Kano

Ma'aikatan sufurin jiragen sama sun rufe harkoki a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an dawo da jigilar sauka da tashin jirage a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

Wannan dai na zuwa ne bayan ma’aikatan sufurin jiragen sama sun hana sauka da tashin jirage a filin jirgin saboda takaddamar da aka samu tsakanin mahukuntan kula da sufuri jirage a kasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, ma’aikatan sun kawo tsaiko ga sauka da tashin jirage sakamakon takaddamar da aka samu tsakanin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) da hukumar gudanarwar filin jiragen sama.

Wani jami’i a filin jirgin ya ce ma’aikatan sun hana tashin jiragen kamfanin sufurin jiragen sama na AZMAN da Max Air zuwa Abuja, inda suka sa aka sauke fasinjoji da suka riga suka hau jirgi.

Aminiya ta gano matakin ya ritsa da wasu gwamnonin da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa da wasu manyan mutane da ke filin jirgin na kokarin ganin an sasanta domin ci gaba da jigilar fasinja.

FAAN da hukumar gudanarwar Filin Jirgi na Malam Aminu Kano sun fara takun saka ne bayan Kungiyar Ma’aikatan Bai Wa Jiragen Sama Hannu (NATCA) sun dakatar da ayyukkansu sakamakon yanke wutar lantarki a filin jirgin da gidan ma’aikatansa.

A ranar Juma’a na FAAN ta yanke musu wuta saboda rashin biyan kudin wutar lantarki.

Ma’aikatan jiragen sama sun shirya gudanar da yajin aiki ranar Juma’a a fadin Najeriya kan sabuwar dokar Sufurin Jiragen Sama (CAA) da ya bai wa Ministan Sufurin Jiragn Sama damar haramta ayyukan kungiyoyin kwadago a bangaren.

A makon jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan dokar daga cikin jerin kudurori shida da Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da su.