✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An buƙaci a sanya sunan Abiola a jerin sunayen Shugabanin Najeriya

A ƙarshen mako nan ne aka gudanar da bikin tunawa da ranar ta 12 ga Yuni a ɗaukacin jihohi 6 na Kudu maso yamma, inda…

A ƙarshen mako nan ne aka gudanar da bikin tunawa da ranar ta 12 ga Yuni a ɗaukacin jihohi 6 na Kudu maso yamma, inda a wasu daga cikin jihohin aka sanya ranar Litinin ta zamo hutu don tunawa da ranar.
A Jihar Ogun, inda a nan ne mahaifar ta Cif MKO Abiola, bikin ya gudana ne ta yadda Mataimakiyar Gwamna Amusu da Sakataren Gwamnatin Jihar suka jagoranci jama’ar garin, suka yi tattaki a kasa daga zauren al’adun gargajiya na June 12 da ke Kuto zuwa gidan iyalan marigayin, a unguwar Oke Ido duk a Abekuta.
A duk ranar 12 ga watan Yuni, al’ummar jihohin Kudu maso yamma kan yi bukukuwan tunawa da zaɓen 12 ga Yuni na shekarar 1993, zaɓan da Cif MKO Abiola ya yi iƙirarin lashewa kuma Gwamnatin Mulkin Soji ta wanccan lokacin a ƙarƙashin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta soke; abin da bai yi wa ɗaukacin Yarbawa da ma ’yan kare tafarkin dimokuraɗiyya daɗi ba.
Ɗan uwan marigayin Alhaji Muhammadu Muritala Olarenwaju, wanda ya yi magana da yawun iyalan gidan Abiola, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sanya sunan Cif MKO Abiola a jerin sunayen shuwagabannin ƙasar nan; domin su ma iyalan gidansa su amfana da alfanun da ake samu a kan haka, la’akari da irin gudunmawarsa dama yadda ya rasa ransa a kan haka. “Akwai wanda riƙon ƙwarya kawai aka ba shi na tsawon wattani 3 amma yana amfanuwa da zamowarsa Shugaban kasa, sai ga shi ɗan uwanmu ya lashe zaɓe an murɗe, an hana masa har ta kai ga ya rasa ransa, sai aka bar iyalansa ba tare wani alfanu ba.” Inji shi.
Alhaji Lekan ɗa ne ga marigayi Cif MKO Abiola, ya shaida wa Aminiya cewa a lokacin da mahaifin nasu ya ƙudiri aniyar tsayawa takarar Shugaban kasa a shekarar 1993, bai samu goyon bayan iyalan gidansa ba, domin gudun irin abin da ya biyo baya inda ya rasa ransa baki ɗaya sai dai a wancan lokacin ya faɗa musu cewa ya fito takara ne domin ya yi gyara a ƙasa.” Mutuwarsa ta haifar mana da babban giɓi, sai dai a yanzu ba abun da za mu yi sai godiya ga Allah duba da yadda malumanmu ke tunawa da irin ayyukan alherin da ya shuka suke yi masa addu’a. Bugu da ƙari, a yanzu mun samu haziƙin gwamna wanda muradin talaka ya sanya a gaba.” Inji shi.