✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An binne Fafaroma Benedict XVI a Birnin Vatican

Za a rika tunawa da shi a matsayin wanda ya taba ajiye mukaminsa cikin sama da shekaru 600

Dubban masu alhini ne suka taru a dandalin St. Peters a Birnin Vatican domin binne Fafaroma Benedict XVI.

Fafaroma mai ci, Francis, shi ne ya jagoranci birne magabacin nasa a ranar Alhamis.

An yi ta busa kararrawa da kade-kaden nuna alhini yayin da aka dauko gawar tsohon jagoran mabiya darikar Katolikan na duniya, yayin da manyan limaman cocin da ke sanye da jajayen riguna suke gefe.

Shugabannin Kasashe da manyan masu rike da sarautun gargajiya daga sassan duniya daban-daban da kuka dimbin masu ibada ne suka yi wa Fadar ta Vatica tsinke, duk da rokon da marigayin ya yi lokacin da yake raye cewa kada a cika yin sharholiya yayin bikin birne shin.

Fafaroma Benedict XVI dai ya mutu me ranar 31 ga watan Disambar 2022 yana da shekara 95 a duniya.

Lokacin da yake raye, ana yi wa marigayin kallon daya daga cikin manyan shugabannin addini na karni na 21, wanda ya sadaukar da akasarin rayuwarsa wajen hidimta wa harkokin coci.

Sai dai za a ci gaba da tunawa da shi a tarihi kan cewa shi ne Fafaroma na farko a cikin sama da shekaru 600 da ya taba sauka daga mukamin nasa saboda tsufa.

%d bloggers like this: