Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun hallaka wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC Bulus Sanda, bayan sun sace shi daga gidansa da ke Mararaba-Rido a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Kwamandar NSCDC a jihar, Babangida Dutsinma shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kaduna ta bakin kakakin hukumar, Orndiir Terzungwe.
“An yi wa marigayin ganin karshe ne a ofishin hukumarmu da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa. Har kyauta aka ba shi a jajibirin ranar da aka sace shi daga bisani kuma a kashe shi”, inji Babangida.
‘Yan bindiga sun kashe makiyayi, sun sace dabbobinsa
Kwamandan ya ce jami’in wanda ya fara aiki da hukumar a shekara ta 2010 ya kasance hazikin ma’aikaci kuma jajirtacce abin koyi.
Daga nan sai ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin tare kuma da kira a jama’ar jihar kan su kara ba jami’an tsaro hadin kai domin tabbatar tsaron rayuka da dukiyoyinsu.