✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bayyana muhimmancin gwajin jini ga ma’aurata kafin aure

Hukumar Asibitin Musulmi da ke danmagaji Zariya ta gabatar da gangamin wayar da kai game da muhimmancin gwajin jini kafin yin aure saboda magance cututtuka…

Hukumar Asibitin Musulmi da ke danmagaji Zariya ta gabatar da gangamin wayar da kai game da muhimmancin gwajin jini kafin yin aure saboda magance cututtuka shida masu saurin yaduwa, musamman ta hanyar jima’i.

An gudanar da taron ne a Lahadin da ta gabata a harabar asibitin kuma wanda ya fara gabatar da kasida ta farko, wani  babban likita ne wanda ya kware a sashen binciken jinni, Dokta Aminu Sirajo Mohammed, wanda ya halarta daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika-Zariya. Ya yi bayani ne a kan irin gwajin jinin da ya kamata a rika yi a kimiyance kafin a yi aure, wato a bangaran likitanci. Ya ce: “Gwajin jini kafin yin aure na da matukar muhimmanci saboda shi aure zama ne na so, aminci da yarda da juna, domin jin dadin zamantakewa, da kuma abubuwan da za su sa rayuwa da juna  ta inganta. Shi ya sa yake da kyau a yi gwaje-gwaje kafin a yi aure, domin ma’aurata su san matsayinsu a lafiya kafin su shiga cikin rayuwar aure. 

Ya kara dacewa: “Tantancewa kafin a yi aure shi ne domin a gano ko mutum na dauke da wani ciwo wanda yake da saurin yaduwa ta fannin jima’i, kamar ciwon kanjamau, Hepatitis B da C da irinsu Syphilis, Gonorrhea da sauransu. Abin da ya sa ake son a sansu saboda su ciwo ne wanda saduwa kan iya kawo su, wato idan wani daga ma’auratan yana dauke da shi. Shi ya sa ake son a yi wannan gwaje-gwajen. Kuma yawancin cututtuka irin wadannan in ban da Syphilis da Gonorrhea su suna warkewa, amma kamar ciwon kanjamau wato cuta mai karya garkuwar jiki, tana da wahalar warkewa, ga kashe kudi kuma ga juya fasalin dan Adam; ka ga ya rame da sauransu. 

Kuma ana yin gwajin ba wai don a hana aure ba ne, sai dai don wadanda suke da shi su sani kuma su shirya idan za su yi aurensu; sun san halin da suke ciki dukkansu, kada daga baya a zo a shiga zargi. Wannan shi ne amfanin yin gwaji kafin aure. Bayan haka kuma yana da amfani mutum ya san ajin jininsa.

Bayan kammala jawabin wayar da kan ne aka gudanar da gwajin jini kyauta ga masu bukata.