✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An bayar da belin wanda ake zargi da satar wayar N36,000 a kan N500,000

An dai gurfanar da matashin ne bisa zarginsa da satar waya salula kirar Itel P36 da darajarta ta kai N36,000.

Wata kotun Majistare da ke zamanta a Ikorodun jihar Legas a ranar laraba ta bayar da belin wani matashi mai shekaru 25 a duniya kan kudi N500,000.

Tun da farko dai an gurfanar da matashin ne bisa zarginsa da satar waya salula kirar Itel P36 da darajarta ta kai N36, 000.

Ana dai tuhumar matashin wanda aka sakaya sunansa da zargin aikata laifuka biyu da suka hada da sata da kuma zamba.

Sai dai Matashin ya musanta laifukan da ake tuhumarsa da su a gaban kotun.

Alkalin kotun, Mai Shari’a T.A. Elias ta bayar da umarnin matashin da ya gabatarwa da kotu mutane biyu da za su tsaya masa tare da biyan kudin belin da aka ambata.

Alkalin ta kuma dage zaman sauraren karar har zuwa ranar 26 ga watan Maris na shekarar 2021.

Tunda farko, dan sanda mai gabatar da kara, ya bayyana wa kotun cewa, an kama matashin da ake zargin ne da aikata laifin a ranar 2 ga watan Febarairun 2021 da misalin karfe 4:30 na dare a unguwan Ojubode a yankin Ikorodu.

Kazalika ya ce shaidawa kotun cewa ko a baya ma an taba kama shi tare da wasu ayarin mutane sun sacewa wani Babatunde kudade.

Aikata wannan laifin a cewar dan sandan ya saba da tanade-tanaden sassa na 411 da 287 na Kundin Manyan Laifuka na jihar Legas na shekarar 2015.