Kwana hudu kafin rufe yin rajista gabanin zaben 2023, ’yan Najeriya da dama da shekarunsu suka kai na zabe a Arewacin Najeriya ba su yanki katin zabe ba.
Alkaluman masu katin zabe da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar sun nuna yankin Kudancin Najeriya ya yi wa Arewa fintinkau wajen yawan masu rajista, duk da cewa Arewa ta fi yawan al’umma.
- DAGA LARABA: Daga Lahadin Nan INEC Za Ta Rufe Yin Rajistar Zabe
- Za a raba wa mata tallafin N20,000 —Sadiya Faruq
- ‘Yan bindiga sun kashe mutum 3 a Katsina
Jihar Legas ce ta daya wajen yawan wadanda suka yi rajista, inda ta yi wa Jihar Kano wadda ta fi yawan al’umma a Najeriya fintinkau — a matsayi na biyu.
Jihohin Delta da Ribas wadanda su ne na uku da na hudu wajen yin rajistar katin zabe kuma sun bar jihohin Kaduna da Sakkwato da Neja da Katsina a baya.
Hakan kuwa ta faru ne duk da cewa, a kwanakin baya, INEC ta kara wa’adinta na rufe rajistar zaben daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa ranar 31 ga watan Yuli.
A wasu jihohin har hutu gwamnatoci suka bai wa ma’aikata domin su samu yin rajistar; Wasu wuraren ibada ma sun wajabta wa mabiyansu yin rajitsar.
A ranar 28 ga watan Yunin 2021 hukumar ta kaddamar da aikin ci gaba da rajistar katin zaben domin sabunta wanda ake da shi gabanin babban zaben 2023.
Amma yanzu da ya rage kwana hudu a rufe, alkaluman Hukumar sun nuna yawancin masu zabe ba su yi ba.
Masu lura da al’amuran yau da kullum sun alakanta matsalar a Arewacin Najeriya da matsalar tsaro da kuma bacin ran masu zabe da kamun ludayin zababbun shugabanni.
Yawan masu zabe
Mutum 84,004,084 ne ke da rajistar katin zabe a Najeriya a lokacin zaben 2019, wanda a lokacin yankin Arewa maso Yamma ke da mafi yawan masu katin — 20,158,100 (24 cikin 100) — a tsakanin yankunan siyasar kasar guda shida.
A lokacin, Kudu maso Yamma ne na biyu da 16,292,212 (19.39%) sai Arewa ta Tsakiya a matsayi na uku da 13,366,070 (15.91%) yankin Kudu maso Kudu kuma 12,841,279 (15.29%).
Arewa maso Gabas na da 11,289,293 (13.44%), sai Kudu maso Gabas mai 10,057,130 (11.97%) a matsayin na karshe.
Masu rajistar zaben 2023
Zuwa karfe 7 na safiyar Litinin, 25 ga watan Yuli da muke ciki, alkaluman INEC sun nuna mutum 11,011,119 sun sabunta rajitsarsu a fadin Najeriya — 7,619,179 sun yi rajista da kansu, sauran 3,391,940 kuma ta intanet.
Jihar Legas ce a kan gaba da mutum 508,936, sannan jihohin Kano a matsayi na biyu, Delta ta uku, ta hudu Ribas, sai Kaduna sannan Bayelsa.
Yadda aka yi wa Arewa fintinkau
Abin mamakin shi ne yadda Legas mai yawan al’umma 12,772,884 ta yi wa Kano mai mutum 14,253,549 fintinkau da kusan mutum 8,000 wajen yawan masu rajistar. Mutum 500,207 ne suka kammala rajista a Kano.
Jihar Delta wadda ta zo ta uku zuwa ranar Litinin na da masu rajisata 481,929 daga cikin yawan al’ummanta 5,307,543.
Wannan adadi da Jihar ta Delta ta samu ya yi wa ragowar jihoihn Arewa fintinkau, duk kuwa da cewa sun fi ta yawan al’umma.
Katsina, na da yawan al’umma 9,300,382 amma mutum 283,470 kacal ne ke da rajista; Jihar Neja mai mutum 6,220,617, kuma mutum 330,453; Sakkwato mai 5,863,187 kuma mutum 293,152 suka kammala rajista.
Kaduna na da masu rajista 417,427 daga cikin yawan al’ummarta 8,324,285, amma Ribas mai yawan al’umma 7,034,973 na da masu rajista 436,459.
A Bayelsa mai yawan al’umma 2,394,725, mutum 416,519 sun yi rajistsa, adadin da ya zarce 323,960 da aka samu a Jihar Filato mai mutum 4,400,974.
Mutum 293,152 na Bayelsa sun wuce 293,152 na Sakkawato mai yawan al’umma 5,863,187, haka zalika 232,525 na Adamawa mai yawan al’umma 4,536,948.
Jihohin da ka samu mafi karancin masu rajistar zu ne Imo (166,835) sai Yobe (134,002) sannan Ekiti (124,844).
A bangaren wadanda suka yi rajista ta intanet, Jihar Osun ce ta zo ta daya da mutum 708,968, sannan Delta (641,765), sai Legas (640,560), Kaduna (574,804) sai kuma Bayelsa (550,208).
Kano na da 369,587; Katsina, 119,137 sai Kebbi, 81,082.
Jerin wadanda suka zo karshe su ne Yobe da mutum 91,239, Enugu mutum 72,167 sannan Imo 71,180.
Dalilin rashin fitowar ’yan Arewa —Fage
Da yake bayani, Masanin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Farfesa Kamilu Sani Fage, ya ce babban dalilin kin fitowa yin rajista a Arewa shi ne rashin gamsuwar mutanen yankin da shugabannin siyasa, musamman masu neman zama magadan Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari a 2023.
Saboda haka suke ganin yin rajistar da ma zaben kansa, babu wani kwakkwaran sauyi da zai kawo.
Abu na biyu a cewarsa, shi ne rashin isasshen wayar da kan jama’a daga bangaren ’yan siyasa da jam’iyya.
Farfesa Fage ya ce ba don kokarin da INEC da kafofin yada labarai da wasu ’yan boko suka yi wajen wayar da kan mutane ba, to da rashin fitowar ta fi haka muni.
Ya bayyana cewa abin takaici ne yadda su ’yan siyasa da za su ci moriyar yawan masu rajistar zabe suka fi mayar da hankali kan abin da za su samu a siyasar cikin gida a jam’iyyunsu, ba su damu da jan hankalin jama’a su yi rajistar zabe ba.
Malamin jami’ar ya bayyana fargabar yiwuwar samun karancin fitowar masu zabe a 2023, idan aka ci gaba da haka wajen rashin wayar da kan jama’a.
Ya bayyana cewa akwai yiwuwar mutane su ki fitowa yin zabe a matsayin nuna bacin ransu da irin kamun ludayin gwamnati ko rashin kyawawan zabi a zaben.
Rashin fitowa alamar rashin yarda ne — Kungiyoyi
A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Sanya Ido kan Mika Gwamnati (TMG) kuma Babban Daraktan Cibiyar Wayar da Kai ta Farar Hula Kan Ayyukan Majalisa (CISLAC), Auwal Musa Rafsanjani, ya ce abin damuwa ne karancin fitowar masu yin rajistar zabe daga Arewa.
Ya kuma alakanta matsalar da rashin tsaro a yankin da kuma gazawar gwamanti wajen magance matsalolin da ke ci wa mutane tuwo a kwarya.
“Yawancin mutane sun yanke kauna da Gwamnatin Buhari saboda gazawarta kan abubuwan da ke faruwa na garkuwa da mutane, talauci, rashin aikin yi da rashawa.
“Wannan babban abin kunya ne ga ’yan Najeriya musamman ’yan Arewa, yankin da Buhari ya fito,” inji Rafsanjani.
Ina mafita?
Rafsanjani babbar mafita ita ce duk masu ruwa da tsaki su yi abin da ya kamata da zai ba wa jama’a kwarin gwiwa game da takun gwamnati gabanin zaben 2023.
“Mutane sun gaji da dadin baki da saba alkwuran shugabannin da ba su damu da abin da ya dami talakawa ba. Ya kamata su rika tuntubar jama’a
“Abu na gaba shi ne a tabbatar wanda ya ci zabe shi aka bai wa; sannan a magance matsalar tsaro tare da tabbatar da kariyar ’yan kasa kafin, a lokacin da kuma bayan zaben, saboda wasu na tsoron fitowa yin zabe.”
A nata bangaren, Shugaban Cibiyar Cigaban Dimokuradiyya (CDD), Idayat Hassan, ta ce gudun hijira, musamman a yankin Arewa maso Yamma na da nasaba da karancin fitowa yin rajistar zabe daga yankin.
Sai dai ta ce, “Sai dai ta ce rashin wayar da kai daga bangaren ’yan siyasa ma ya taka rawa. Ya kamata a yi amfani da kwanakin da suka rage wajen yawar da kan mutane.”
Duk wanda ya yi rajista sau biyu to ya sara —INEC
Kwamishinan INEC na Abuja, Yahaya Bello, ya ce wa’adin rufe rajistar zaben shi ne ranar Lahadi 31 ga watan Yuli mai karewa.
Ya kuma bayyana cewa duk wanda wanda ya yi rajistar katin zabe sau biyu, to shi ke nan ya rasa, dukkansu.
Bello ya ce za a dakatar da duk abubuwan da suka danganci rajistar katin zaben ranar 31 ga Yuli, 2022, sin kuma batun katuna.
Sai ya bayyaan cea za a kara lokacin tashi aikin zuwa karfe 5 na yamma, har a ranakun Asabar da Lahadi.
Hakan da ya ce za a yi kafin rufewar zia ba da damar yi wa karin mutane rajistar, saboda lokaci ya riga ya kure.
Daga: Sagir Kano Saleh, Abdulaziz Abdulaziz, Abbas Jimoh (Abuja) & Clement Oloyode (Kano)