Wasu ‘yan bindiga sun bankawa hekta 250 ta gonar shinkafar Gwamnan jihar Benuwai Samuel Ortom.
Gonar shinkafar tana mahaifar Gwamnan ne a unguwar Gbajimba a karamar hukumar Guma jihar Benuwai, shinkafar da aka kona zata kai adadin kudi na Naira miliyan 100.
Manajan gonar Kena Iordzua, ya nuna wa manema labarai wuraren da aka kona kuma ya ce, wadanda suka kona gonar suna kusa da gonar kwanaki kadan kafin su shiga gonar da shanunsu, su bankawa gonar wuta . Ma’aikatan gonar sun yi kokarin kashe gobarar amma abin ya citura saboda lokacin hunturu.