An bankado sansanoni uku na ba wa ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB horo kan aikin soji, tare da cafke wani kwamandan kungiyar.
Jami’an ’yan sun bankado manyan sansanonin da IPOB ke ba wa dakarunta horo ne a yankin Atta a Ikeduru, Izmobie a Oguta da daya a Karamar Hukumar Ideato ta Arewa, a Jihar.
“An gano tarin makamai, motocin sata, ababen fashewa, harsasai, garin bindiga, buhunan tabar wiwi, da sauran miyagun kwayoyi da kuma layu, tutocin lPOB/ESN, a wurin,” inji Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo.
Ta ce rundunar dabaru na musamman ce ta bankado sansanin na IPOB a yayin aikinta na yaki da ta’addanci a jihar.
Kakakin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CSP Mike Abatam, ya tabbatar da cafke Kwamandan IPOB, wanda a wurin bincike ya ba da bayanan da suka kai ga gano sansanin daukar horon kungiyar.
A cewarsa, da ganin jami’an tsaro, sai ’yan haramtacciyar kungiyar a-waren suka bude musu wuta, inda aka dauki lokaci ana gwabza fada.
“Karfin makaman ’yan sanda ya ci karfinsu, inda wasu da dama daga cikinsu suka tsere da raunukan harbi a jikinsu.
“Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Abutu Yaro, ya jinjina wa jami’an ’yan sandan kan namijin kokarin da suka yi, sannan ya sha alwashin yaki da ta’addanci a Jihar Imo,” cewar sanarwar.