Wasu da ake kyautata zata hayar su aka dauka sun banka wa ginin Majalisar Dokokin Jihar Ribas wuta da tsakar daren Lahadi.
Rahotanni sun ce an cinna wa majalisar wuta ne a daidai lokacin da ake zargin ta fara shirye-shiryen tsige Gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara.
- Kudaden aikin da ake ba ’yan majalisa sun yi kaɗan – NILDS
- An lakada wa Fasto da ɗan cocinsa duka kan zargin satar mazakuta
Majiyoyin da ke da kusanci da majalisar sun shaida wa wakilinmu cewa bata-garin sun kutsa kai cikin majalisar ce sannan suka banka mata wuta a kokarinsu na hana yunkurin tsige Gwamnan a ranar Litinin.
Sai dai wakilinmu ya gano cewa sauƙin da jami’an kashe gobara suka kai cikin gaggawa ya taimaka wajen kashe wutar don kar ta cinye ilahirin ginin majalisar.
Kokarin wakilin namu na jim ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe Koko, a kan lamarin ya ci tura.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da bayanai ke nuna cewa alaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Fubara da maigidansa, tsohon Gwamnan Jihar kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike.