✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Bakado Shirin ISWAP Na Kai Hari A Abuja Da Wasu Jihohi

Wuraren sun hada da jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna da kuma Kogi.

Kungiyoyin ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP na shirin kai hari a Abuja da Legas da wasu jihohi Arewacin Najeriya.

Bayanin harin da kungiyoyin ke kitsawa ya fito ne daga wata ta wasikar sirri da hukumar tsaro Civil Defence ta aika wa dukkannin ofisoshinta a ranar 25 ga watan Yulin da muke ciki.

Wasikar na dauke ne da sa hannun Mataimakin Shugaban Rundunar mai lura da aikace-aikace, DD Mungadi.

Wakilinmu ya samu ganinta a ranar Talata, kuma a ciki ta lissafa jihohin da kungiyoyin ke shirin kai wa hari da suka hada da Abuja da Legas da Katsina da Zamfara da Kaduna da kuma Kogi.

Mataimakin Shugaban Civil Defence ya umarci jami’ansa na dukkanin jihohi da su tsaurara matakan tsaro a duk muhimman wurare da kuma kadorin gwamanati a jihohinsu.

A cewar takaradar, “Wadannan wurare sun hada da makarantu da wuraren ibada da kuma kadarori masu muhimmanci a jihohinku, domin kare su daga harin bata-gari.

“Ku dauki wannan umarni da matukar muhimmanci tare da aiwatarwa cikin gaggawa”, a cewar wasikar.

Da aka tuntubi kakakin rudunar ta Civil Defence, Shola Odumosu don karin hakse, ya musanta cewa kwarmata wannan wasika ba daga wurinsu ba ne.