Aƙalla wasu tsofaffin ’yan bindiga shida masu garkuwa da mutane sun karɓi takardar shaidar tuba a Ƙaramar Hukumar Gulani ta Jihar Yobe.
Aminiya ta ruwaito, tubabbun ’yan ta’addan su ne waɗanda a baya suka hana mazauna sakat a wasu ƙananan hukumomin Yobe sanadiyyar saboda ta’azzarar garkuwa da mutane da kuma fashin daji da suke yi.
- An kama matashi kan luwaɗi da yara 12 a Jigawa
- Ƙudirin Dokar Haraji ya tsallake karatun farko a Majalisar Dattawa
Shugaban Karamar Hukumar Gulani, Dayyabu Iku Njibulwa ne a hukumance ya karɓi tubabbun ’yan bindigar waɗanda wata Babbar Kotun Shari’a ta wanke daga ta’addancin garkuwa da mutane.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, waɗanda suka halarci taron karɓar tubabbun ’yan ta’addan akwai manyan jami’an tsaron yankin da suka haɗa ’yan sandan, DSS da Sibil Difens da kuma Alƙali Kotun Shari’ar haɗi da Shugaban Ƙungiyar Masu Unguwanni na Ƙaramar Hukumar Gulani da sauransu.
Da yake jawabi, Shugaban Ƙaramar, Dayyabu Njibulwa, ya hori tubabbun ’yan ta’addan da kotu ta wanke kan sake gina rayuwarsu bisa tafarkin addini da kuma tanade-tanaden na al’ada.
Njibulwa ya kuma buƙaci al’umma da su karɓi tubabbun ’yan ta’addan da hannu biyu, yana mai shawartar duk masu irin mummunar ɗabi’a da su ma su tuba su rungumi zaman lafiya.
A cewarsa, gwamnati a kodayaushe tana cikin shirin karɓar duk wani ɗan ta’adda da duk wasu masu aikata miyagun laifuka da ke sha’awar yin tuba na haƙiƙa.
Bayanai sun ce Kotun ta karɓi tuban ’yan ta’addan bayan ta gamsu da nadamar da suka nuna kan miyagun laifukan da suka aikata, inda suka yi rantsuwa da Alƙura’ni domin tabbatar wa alƙali da sauran al’umma sun yi watsi da duk wani mugun nufi.
Alƙalin ya yi wa al’umma gargaɗi tare da hani kan nuna duk nau’i na ƙyama da zai fusata ’yan ta’addan da suka tuba.
Ɗaya daga cikin tubabbun ’yan ta’addan da ya yi magana a madadin sauran a yayin taron, ya ce suna nadamar duk wasu miyagun ayyukan da suka aikata yana mai ba da tabbacin cewa za su jajirce wajen kasancewa jakadun zaman lafiya da ci gaban ƙaramar hukumar da kuma Jihar Yobe baki ɗaya.