Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce Gwamnatin Tarayya ta bai wa kowanne gwamnan jiha naira biliyan 30 domin rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwar da suke fuskanta.
Akpabio ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar na ranar Talata, a ci gaba da tattauna irin halin ƙuncin da jama’ar kasar suka samu kansu a ciki, wanda ake dangantawa da cire tallafin mai.
- Za a binciki Gwamnatin Buhari kan bashin naira tiriliyan 30 da ta karɓo a CBN
- EFCC ta tsare ’yan canji a Kasuwar WAPA
Shugaban majalisar ya ce ya samu wadannan bayanai ne daga wajen Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Kasa wadda ta miƙa wa jihohin waɗannan kuɗaɗen da ake magana a kansu.
Akpabio ya ce waɗannan kuɗaɗen daban ne da naira biliyan bib-biyu da aka bai wa gwamnonin a watan Satumbar bara daga cikin biliyan biyar-biyar na rancen samar wa jama’ar su tallafin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Shugaban majalisar ya bai wa gwamnonin shawara wajen yin amfani da waɗannan makudan kuɗaɗe ta hanyar da ta dace domin ganin jama’ar jihohin su sun samu tallafin da ya dace, musamman a bangaren abin da ya shafi abinci.
Akpabio ya ce ana iya cimma nasarar gabatar da tallafin ne ta hanyar amfani da shugabannin kananan hukumomi saboda kusancin su da mutanen da ke yankunan karkara.
Shugaban majalisar wanda ya yi Allah wadai da zanga-zangar da aka gani a wasu jihohin kasar da ake danganta su da tsadar rayuwa, ya zargi ‘yan adawa da daukar nauyin su, duk da kokarin da ya ce Majalisar Dattawan na yi domin tunkarar matsalar tare da Gwamnatin Tarayya.
Akpabio ya ce babu wani mahaifin da ke fatar ganin ɗansa ya kwanta ba tare da ya ci abinci ba, saboda haka ya buƙaci takwarorinsa da su mayar da hankali a kan ɗaukar matakin samo abinci duk inda yake domin wadata jama’a.