Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta samu karin makamai da kayayyakin aiki na musamman don shirya wa yanayin zaben Gwamna da na ’yan Majalisun Jihohi.
Daga cikin kayayyakin dai akwai motocin silke da wasu kayayyaki na kariya da aka turo daga hedkwatar rundunar ta kasa da ke Abuja.
- Kano: Gamayyar kungiyoyin Tijjaniya sun bukaci a zabi Abba Gida-Gida
- Sojoji sun cafke ’yan Boko Haram 900 a dajin Sambisa
Wannan batu na dauke ne a wata sanarwa mai dauke da sanya hannun Kakakin rundunar a Jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Oqua Etim.
Sanarwar ta ce Kwamishinan ya kuma ba da umarnin a raba kayayyakin ga Turawan ’yan sanda (DPO) da kuma rundunoni na musamman don aiki da su yadda ya kamata a lokacin zaben.
Kwamishinan ya kuma jinjina wa kokarin jami’ansa kan yadda suka gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ’yan majalisar tarayya, inda ya hore su da su sake zama yan ba ruwa na a harkar siyasa.
Ya kuma tabbatarwa al’umma cewa za su kare rayuka da dukiyoyinsu, sannan ya gargadi masu yunkurin ta da hankali da su shafa wa kansu ruwa a lokacin zaben saboda jami’ansa za su hada kai da sauran jami’an tsaro dan tabbatar da doka da oda.