✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…An ba ‘yan Najeriya diyyar miliyan 1 a Saudiyya

Gwamnatin Saudiyya ta nemi afuwar wasu mahajjatan Najeriya biyu da jami’an tsaro suka ci zarafinsu a filin jirgin sama na Madina. Mataimakin gwamnan yankin Madina,…

Gwamnatin Saudiyya ta nemi afuwar wasu mahajjatan Najeriya biyu da jami’an tsaro suka ci zarafinsu a filin jirgin sama na Madina.

Mataimakin gwamnan yankin Madina, Sheikh Mohammad Albijawi, wanda ya mika wa wadanda abin ya shafa wasikar, ya tabbatar musu da cewar za a hukunta jami’an tsaron da suka aikata laifin kamar yadda BBC ta ruwaito.

Saudiyyar ta kuma bai wa mutanen diyyar riyal dubu biyar ga ko wanne daya daga cikinsu, wanda ya kama naira dubu 500 kenan ga duk mutum daya.

Ya yi kira ga mahajjatan Najeriya su kasance masu halayya mai kyau, kuma su gudanar da aikin hajin kamar yadda dokokin addini suka tanadar.

Ya bayyana cewar hukumomin Saudiyya sun samar da ababen more rayuwa da za su sa a gudanar da aikin hajjin bana ba tare da matsala ba.

Jakadan Najeriya a Saudiyya, Umaru Salisu, ya yaba wa hukumomin Saudiyya kan yadda suka mayar da martani game da lamarin cikin gaggawa.

Mahajjatan da aka ci zarafinsu Audu Damina Muhammad da Ibrahim Nani Godi sun gode wa hukumomin Saudiyya da hukumar jin dadin alhajan Najeriya game da irin matakan da suka dauka kan abin da ya faru da su.