✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba wa mata 3,400 jarin N20,000 a Edo

Gwamantin Tarayya ta gwangaje matan karkara 3,400 da jarin N20,000 a jihar Edo.

Gwamnatin Tarayya ta raba wa mata 3,400 jarin N20,000 kowacce, karkashin shirin na yaki da talauci a tsakanin mutanen karkara.

Da take jawabi yayin bikin raba kudaden, Ministar Agaji da Walwalar Al’umma, Sadiya Umar Farouk, ta ce rabon jarin na daga cikin tsarin bunkasa hanyar shigar kudaden mutanen karkara.

Ministar wadda ta samu wakilcin Darakatan Walwalar Jama’a na Ma’aikatar, Ali Grema, ta ce, “Manufarmu ta ce tallafa wa mabukata 3,400 a kananan hukumomin Jihar Edo, kuma muna sa ran jarin zai habaka hanyar shigar kudaden wanda suka amfana.”

Ministar ta ce Gwamnatin Tarayya tana kokarin ci gaba da yakice mutane miliyan daya daga cikin halin kangin talauci, duk da matsalar kudin shiga da take fuskanta.

Kazalika, ta ce ana sa ran jarin na N20,000 da aka ba wa matan jihar, zai taimaka gaya wajen samar musu da kudaden shiga.

A nata bangaren, mai dakin Gwamnan Jihar Edo, Betsy Obaseki, ta yaba wa Shugaba Buhari kan yunkurin da yake yi na raba ’yan Najeriya daga kangin talauci.

Deborah Onaluwa, wadda ta wakilci daukacin wadanda suka amfana da tallafin, ta gode wa Gwamnatin Tarayya, tare da alkawarin amfani da kudaden wajen habaka kasuwancinsu.