Gwamnatin Kasar Saudiyya ta nada Dokta Hanan Bint Abdulrahman bin Nutlaq al-Ahmadi a matsayin mace ta farko mai rike da babban mukami a Majalisar Shura ta kasar.
Sarkin Salman bin Abdulaziz, ya nada Dokta Hanan a matsayin Mataimakiyar Shugaban Majalisar Shura.
- An gano takun sawun mutane da ya shekara dubu 120 a Saudiyya
- Kwanan nan za a dawo da aikin Umarah —Saudiyya
Dokta Hanan daya ce daga cikin mata 30 na sahun farko da aka shigar cikin Majalisar Shura shekara bakwai da suka gabata, kuma mukamin da aka ba ta a yanzu shi ne na uku mafi girma.
Nadin da aka yi wa Dokta Hanan a makon jiya ya biyo bayan wasu sauye-sauye da Sarki Salman ya gudanar a manyan hukumomin kasar ciki har da Majalisar Shura da sauran hukumomin addini.
A shekarar 2013 ne gwamnatin Saudiyya karkashin jagorancin marigayi Sarki Abdallah Bn Abdulaziz AlSaud, ta kaddamar da kudurin sabuwar doka wadda ta amince a bai wa mata kashi 20 cikin 100 na kujerun Majalisar Shura guda 150.
Bisa al’ada a kasar Saudiyya, ’yan Majalisar Shura ne ke da alhakin gabatar da dokoki domin amincewar Masarautar.