✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashe-kashe: ‘Mutanen Filato su tashi su kare kansu’

Majalisa ta ba Gwamna Lalong mako biyu ya dau kataki kan masu kisan gilla.

Majalisar Dokokin Filato ta ce mutanen Jihar su tashi su kare kawunansu daga maharan da ke aikata kisan gilla da ke tayar da zaune tsaye a Jihar.

Majalisar Filato, ta bakin Shugaban Kwamitin Yada Labaranta, Dasun Phili Peter, ta ce tunda jami’an tsaro sun kasa kare mutanen jihar, to ya zama wajibi mutane su tashi tsaye su kare kawunansu.

Majalisar ta kuma ba wa Gwamna Simon Lalong mako biyu ya dauki matakin kawo karshen kashe-kashe a Jihar ko kuma ta dauki nata irin matakin.

Shugaban Kwamitin ya ce Majalisar ta ba wa gwamnan mako biyun ya  tabbatar ya aiwatar da shawarwarin ta bayar kan yadda za a dawo da zaman lafiya a jihar, idan kuma ya ki Majalisar za ta dauki matakin da ya dace.

Ya bukaci jami’an tsaro a jihar ta Filato da su zakulo wadanda suka aikata kisan gilla a jihar domin hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Peter, ya jajanta wa gwamnati da jama’ar Jihar ta Filato kan kisan gilla da aka yi a kananan hukumomin Bassa da Barikin Ladi da Bokkos da  Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Mangu da Riyom da Yelwa Zangam da kuma Jami’ar Jos.

Da yake yin tir da duk kisan gillan da aka yi a Jihar, Peter ya ce Majalisar ba za lamunci hakan ba, sannan ya aike da sakon ta’aziya ga iyalan wadanda aka kashe.

Tun a makon da ya gabata ne rikici ya ci gaba yin kamari a jihar ta Filato, inda aka kashe wasu matafiya kusan 30 a kan hanyarsu daga Bauchi zuwa Jos.

Kasa da mako biyu bayan nan aka kai wa wani kauye hari, inda aka kashe kusan mutum 30, ciki har da wadanda aka kona su da ransu.

Hare-haren sun tayar da hankula a sassan jihar, wanda har ya sa gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita gaba daya a kananan hukumomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa.