Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta bayar da tallafin Naira miliyan ɗaya ga iyalan DPO ɗin da wani soja ya harbe a Jihar Zamfara.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar a wannan Juma’ar ce ta bayyana hakan.
- Yadda aka daƙile shirinmu na sayar da buhun siminti N3,500 — BUA
- An sauya ranar zaɓen ƙananan hukumomin Kano
SP Abubakar ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Kebbi, Bello M. Sani a madadin jami’an rundunar ne ya bayar da tallafin ga iyalin DPO ɗin su soma rage raɗaɗi kafin karɓar haƙƙoƙin marigayin.
Sanarwar ta ce Kwamishinan da tawagarsa sun ziyarci garin Gombi da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko ta Jihar Sakkwato domin jajanta wa iyalan mamacin.
Ana iya tuna cewa, a ranar Laraba ce wani soja ya sa bindiga ya harbe wani DPO ɗin ’yan sanda a wani shingen binciken ababen hawa a Jihar Zamfara.
Wata sanarwa da rundunar ’yan sandan Zamfara ta fitar a ranar Alhamis, ta ce lamarin ya faru ne a garin Ɗanmarke da ke karƙashin Ƙaramar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara da misalin ƙarfe 10:30 na ranar Laraba.
SP Halliru Liman wanda shi ne DPO na Wasugu da ke Jihar Kebbi ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa ta halartar taronsu na wata-wata, inda sojojin da ke ƙarƙashin rundunar Hadarin Daji suka tsayar da shi a wani shingen bincike.
“Duk da cewa ya bayyana musu cewa shi ɗan sanda ne kamar yadda suka buƙata amma kuma sai kawai wani soja mai suna Hassan ya zaro bindiga ya harbe SP Liman a kansa, abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa,” in ji sanarwar.
Rundunar ’yan sandan ta Jihar Zamfara ta nemi da dukkan hukumomin da ke da ruwa da tsaki da su gudanar da cikakken bincike na yadda al’amarin ya faru.
“Abin da sojojin suka yi ya fito fili da irin rashin son aiki tare da sauran jami’an tsaro wanda kuma ba za mu lamunta ba,” kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.