Gwamnatin Jihar Gombe, ta karrama Hajara Ibrahim Dan’azumi, mai shekara 19 wacce ta lashe musabaƙar karatun Alkur’ani ta Duniya kyautar kujerar aikin hajji da kudi Naira miliyan biyar.
Da yake mika wa matashiyar cakin kudin, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce Hajara ta taka rawar ganin tare da daga dajarar Gombe a idon duniya.
- Gwamnan Filato Ya Sa A kamo Wadanda Suka Kashe Makiyayi
- Ranar Mata ta Duniya: Gwamnatin Kano za ta tallafa wa mata 100 da sana’o’i
Tun da fari gwamnan ya yi alkawarin karrama duk wanda ya lashe gasar daga Najeriya.
Ya ce matashiyar ta cancanci a karrama ta, wanda gefe guda ya bai wa makarantar da ta koyon karatun Alkur’ani kyautar miliyan biyar.
Da yake magana a madadin iyayen Hajara da kuma malaman makarantar matashiyar, shugaban makarantar, Farfesa Sheikh Dahir Inuwa, ya ce Hajara ta yi karatu a makarantu daban-daban kafin zuwa makarantar Abubakar Sadiq.
Ya ce a makarantar ta fara karatu a Darur Arqam da Imam Malik sannan ta dawo Abubakar Sadiq, kuma malamai biyar ne suka gwada karfin haddarta kafin zuwanta musabaƙar.
Kazalika, ya ce akwai ’yan uwanta da kuma ita da suke da bai war haddar Al’kur’ani.
Gwarzuwar ta shaida wa Aminiya cewar tana cikin farin cikin wanda ba zai misaltu ba.
Sannan ta yi kira ga sauran dalibai da suka fafata da kada su yi kasa a guiwa wajen zage damtse da samun nasara a gaba.