✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba dan sanda kujerar Hajji da N250,000 saboda mayar da dalolin tsintuwa

Wani dan sandan Najeriya ya samu tukwicin kujerar aikin Hajji da tsabar kudi Naira 250,000 saboda ya mayar da Dala 800 da ya tsinta mallakar…

Wani dan sandan Najeriya ya samu tukwicin kujerar aikin Hajji da tsabar kudi Naira 250,000 saboda ya mayar da Dala 800 da ya tsinta mallakar wata maniyyaciya a Katsina.

Mawallafin jaridar intanet ta Katsina City News, shi ne ya yi wa Nura Mande kyautar kudin a ranar Alhamis domin yaba masa kan halin da’ar da ya nuna wajen maido da kudin da ya tsinta.

Wata maniyyaciya ce dai ta batar da kudin ga guzurinta a sansanin alhazai na Jihar Katsina yayin shirye-shiryen aikin Hajjin da ya gabata.

Dan Majalisar Dokokin Katsina, Alhaji Ali Abu-Albaba ne ya jagoranci mika kyautar ga Mande a madadin mawallafin jaridar a Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Katsina.

Abu-Albaba ya ce jaridar ta yanke shawarar kyautata wa dan sandan ne saboda gaskiyar da ya nuna.

Yana mai cewa, “Ba kowa ne zai tsinci irin wannan kudi a wurin da babu wanda ya gan shi sannan ya mayar wa mai shi ba.”

Abu-Albaba ya ce baya ga wannan tukwicin da dan sandan ya samu, an kuma samu wanda ya biya masa kujerar Hajji don sauke farali badi idan Allah ya kai mu.