Wani dan sandan Najeriya ya samu tukwicin kujerar aikin Hajji da tsabar kudi Naira 250,000 saboda ya mayar da Dala 800 da ya tsinta mallakar wata maniyyaciya a Katsina.
Mawallafin jaridar intanet ta Katsina City News, shi ne ya yi wa Nura Mande kyautar kudin a ranar Alhamis domin yaba masa kan halin da’ar da ya nuna wajen maido da kudin da ya tsinta.
- Mun kashe Triliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati —Malami
- Na hannun daman Amaechi ya sauya sheka zuwa PDP
Wata maniyyaciya ce dai ta batar da kudin ga guzurinta a sansanin alhazai na Jihar Katsina yayin shirye-shiryen aikin Hajjin da ya gabata.
Dan Majalisar Dokokin Katsina, Alhaji Ali Abu-Albaba ne ya jagoranci mika kyautar ga Mande a madadin mawallafin jaridar a Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Katsina.
Abu-Albaba ya ce jaridar ta yanke shawarar kyautata wa dan sandan ne saboda gaskiyar da ya nuna.
Yana mai cewa, “Ba kowa ne zai tsinci irin wannan kudi a wurin da babu wanda ya gan shi sannan ya mayar wa mai shi ba.”
Abu-Albaba ya ce baya ga wannan tukwicin da dan sandan ya samu, an kuma samu wanda ya biya masa kujerar Hajji don sauke farali badi idan Allah ya kai mu.