✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An aika maharan da suka kashe ’yan sanda lahira a Anambra

’Yan sandan sun kawar da maharan tare sa kwato makamansu.

’Yan Sanda a Jihar Anambra ta kashe wasu ’yan bindiga biyu da suka kashe ’yan sanda biyu a ranar 29 ga watan Disamba, 2023.

Kwmashinan ’yan sandan jihar, Aderemi Adeoye ya shaida wa Kamfanin Dillancin labaran Najeriya (NAN) a Awka ranar Litinin, cewa an kawar da ’yan bindigar ne a wani samame da suka kai sansaninsu da ke Ogboji, Karamar Hukumar Orumba ta kudu, a ranar Lahadi.

Adeoye ya ce an ceto wani mutum mai shekara 51 da aka yi garkuwa da shi a cikin wata motar kirar Lexus Jeep.

Ya ce sauran abubuwan da aka kwato daga hannun maharan sun hada abubuwan fashewa guda hudu, bindigogi guda biyu da harsasai 16.

Adeoye ya ce za a ci gaba da farautar maharan da duk wani mai aikata laifia jihar.

Ya sake jaddada kudurin tabbatar da tsaron kowa, sannan ya bukaci mazauna jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da fargaba ba.