Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta ce, wasu mutane sun kashe wasu mutum biyu da ake zargi da fashin babur, ta hanyar yi musu dukan kawo wuka kuma suka kona gawar mutum guda daga cikinsu, a Karamar Hukumar Misau da ke jihar.
Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil ya ce, mutanen garin sun zargi mutanen ne da kashe wani matashi mai suna Muhammad Mamuda Baba Jibir mai shekara 25, inda aka tsince shi an yanke sassan jikinsa, bayan sace babur dinsa aka jefar da gawarsa.
- Abuja: Yadda mutane ke kwana a cikin motoci da gine-ginen da ba a kammala ba
- Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri ya yi murabus
Wakili ya ce, ’yan sanda a Misau sun samu labarin fashi da makamin da kisan gilla a ranar 18 ga Agustan 2024 da misalin karfe 10:00 na dare, inda aka shaida musu an ga wata gawa kwance cikin jini a ungwar Agwaluma a wajen garin Misau.
Ya ce, DPO din karamar hukumar ya jagoranci ’yan sanda zuwa wajen da lamarin ya faru, inda suka gano an yanke makogwaron wanda abin ya shafa.
“Jami’an tsaro sun kai gawar zuwa Babban Asibitin Misau, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa,” in ji shi.
’Yan sandan sun ce, Muhammad Mamuda Baba Jibir dan unguwar Sabon Layi ne a garin Misau da ke sana’ar acaba da babur.
“Wadanda ake zargin ’yan fashi da makami ne suka kwace babur dinsa kirar Boxer, suka tafi da shi, inda aka miƙa gawarsa ga ’yan uwansa domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
“Sa’o’i 24 da faruwar lamarin, ’yan sanda sun kama mutum biyu a kan babur din marigayin a hanyar Misau zuwa Kari, inda wasu mutane da suka fusata suka ci ƙarfin ’yan sanda suka kashe tare da ƙone gawar ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin,” in ji shi.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Auwal Musa Mohammed ya nuna takaici kan yadda matasan suka fusata, suka yi wa wadanda ake zargin kisan gilla bayan ’yan sandan sun kama su.
Ya ce, “sun rinjayi ’yan sanda, inda suka kwace su daga hannun ’yan sanda, suka kashe su, hakan ya saba wa dokokin kasa.”
Kwamishinan ya gargadi mazauna jihar cewa, rundunar ba za ta lamunci wasu daga cikin jama’a su ci gaba da daukar doka a hannunsu ba, ta hanyar kashe wadanda ake zargi da aikata laifi.