✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ƙara mafi karancin albashin Kaduna zuwa N72,000

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya sanar da Naira 72,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Gwamna Uba Sani ya sanar da Naira 72,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Jihar Kaduna.

Da haka Kaduna ta zama ta 18 a jerin jihohin da suka sanar da ƙarin mafi karancin albashin ma’aikatansu.

Gwamnan ya sanar da haka ne a ranar Alhamis, yana mai cewa hakan ya yi daidai da manufar gwamnatinsa na kula da jin dadin ma’aikata.

Ya ci gaba da cewa gwmanatinsa za ta samar da motoci 100 masu amfani da iskar gas na CNG domin sauƙaƙa harkar sufuri.

Ya bayyana cewa za a yi amfani da motocin ne wajen zirga-zirgar ma’aikata, ƙarƙashin kulawar kungiyoyin ƙwadago