✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ƙaddamar da gidan rediyon EFCC mai yaƙi da labaran ƙarya

Gwamnatin Tarayya da EFCC sun ɗaura ɗamarar yaƙi da labaran ƙarya a Nijeriya.

Gwamnatin Tarayya da Hukumar Yaƙi Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, sun sha alwashin daƙile yaɗuwar labaran ƙarya a Najeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Jama’a, Mohammed Idris da shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ne suka bayar da wannan tabbacin yayin da suke ƙaddamar da gidan rediyon EFCC da ke kan mita 97.3 a zangon FM a Abuja a hukumance.

Idris ya ce kamata ya yi a yaba wa hukumar kan yadda take yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma samun sakamako mai kyau.

Ministan ya ƙara da cewa babu wani ɗan Najeriya a yau da zai yi watsi da su ko ya musanta ko kuma ya yi watsi da tasirin da EFCC ke yi.

Ya kuma yaba da shirin gidan Rediyo da hukumar ta yi, inda ya bayyana cewa za a ba ta cikakken ikon yaƙi da labaran ƙarya, daƙile yaɗuwar jita-jita wanda hakan zai rubanya ƙoƙarin da take a ayyukanta.

Ya kuma bai wa hukumar EFCC tabbacin samun ƙarin goyon baya da haɗin gwiwa a ayyukan gidan rediyo da sauran ayyukan hukumar.

A nasa ɓangaren, Olukoyede wanda ya hikaito muhimmancin ƙirƙiro gidan rediyon hukumar, ya bayyana ƙaddamar da gidan rediyon da hukumar ta yi a matsayin wani muhimmin mataki.

Shugaban na EFCC ya yi Allah-wadai da yadda labaran ƙarya ke gurgunta ayyuka hukumar da kuma rage wa ma’aikatanta karsashi da ƙwazon aiki, inda ya ce samar da gidan rediyon zai taimaka wa hukumar wajen fitar da labaranta na haƙiƙa da gaskiya.

Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa mai yaƙi da cin hanci da rashawa, Sanata Emmanuel Udende, ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin wani abun ban tsoro da ke gurgunta ci gaban ƙasa.