Gwamnatin Amurka na shirin rage wa’adin shekarun biza da ake bai wa daliban kasashen waje masu zuwa kasar karatu zuwa shekara hudu.
A bukatar da Ministan Tsaron Cikin Gida ya nema, Ma’aikatar Harkokin Waje ta nemi a rage wa’adin bizar daliban da suka fito daga kasashen da ake goyon bayan ta’addanci zuwa shekara biyu.
- Amurka ta haramta kayan China kan musguna wa Musulmi
- Amurka ta sa wa masu magudin zabe a Najeriya takunkumi
Dangane da dokar, yanzu daliban da ke zuwa karatu a Amurka za su iya zama a kasar har sai sun kammala karatunsu.
Idan aka tabbatar da rage wa’adin bizar, dalibai ’yan kasashen waje za su rika neman karin wa’adi ne idan ba su kammala karatunsu cikin shekara hudu ba, ko kuma suna da rashin lafiya ko kuma in sun samu wani dalili mai karfi na zama a kasar.
Bisa sabon tsarin, za a rika bai wa dalibai biza ne a rukunan ‘F’ da ‘J’ da kuma ‘I.’