✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amurka za ta ‘kaurace’ wa gasar Olympics saboda cin zarafin Musulman Uighur a China

Sai dai kauracewar iya jami’an gwamnati ta shafa, ban da ’yan wasa.

Kasar Amurka ta sanar da janyewar jami’an gwamnatinta daga gasar Olmpics da za a yi a birnin Beijing na kasar China, bisa zargin take hakkin bil-Adaman da take yi wa gwamnatin Chinan.

Fadar White House a ranar Litinin ta ce ba za ta aike da wakilci zuwa gasar ba don nuna rashin amincewarta ta yadda kasar ke take hakkin Musulmi ’yan kabilar Uighur da ke yankin Yammacin Xinjiang na kasar.

Sai dai kauracewar iya jami’an gwamnati kawai ta shafa, ban da ’yan wasan da za su wakilci kasar.

Sakataren Yada Labarai na Fadar ta White House, Jen Psaki, ya shaida wa ’yan jarida cewa, “Gwamnatin Shugaba Joe Biden ba za ta tura kowanne irin wakilicin jami’in gwamnati ko na diflomasiyya zuwa gasar Olympics ta shekarar 2022 da za a yi a birnin Beijing na kasar China ba.

“Hakan ya faru sakamakon yadda gwamnatin ke ci gaba da kisan kiyashi tare da aikata laifukan yaki a yankin Xinjiang.

“Jami’an huldar diflomasiyyar Amurka ba za su dauki wannan batunda wasa ba kamar yadda suka saba, ba za mu yi hakan ba,” inji Fadar White House.

To sai dai Amurka ta bayyana matakin a matsayin na siyasa.

Ko a ranar Talatar da ta gabata ma, kasar Birtaniya ma ta ce za ta duba yiwuwar kaurace wa gasar a nan gaba.

“An tambaye ni ko za mu je ko a’a, za mu yanke shawara a kan haka,” inji Mataimakin Firaministan Birtaniya, Dominic Raab.

Sai dai Sakataren na Fadar White House ya ce kauracewar jami’an gwamnatin na Amurka ba zai shafi ’yan wasan kasar ba, wadanda ya ce suna da cikakken goyon bayan Shugaba Biden.