Amurka ta amince ta dawo wa Najeriya kimanin Dala miliyan 53 daga cikin kuɗaɗen sata da ta ƙwato daga tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke.
An ƙwato kuɗaɗen da kadarorin da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 80 ne a jihohin New York na ƙasar Amurka, inda Diezani ta ke fuskantar bincike kan kwanciyar magirbi kan dukiyar gwamnati.
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya da Amurka sun amince a dawo wa Najeriya kuɗaɗen ne bisa sharaɗin amfani da su wajen aikin samar da wutar lantarki da kuma yaƙi da ta’addanci a Najeriya.
Kakakin Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ta sanar a ranar Asabar cewa, “kasasshen biyu sun amince a dawo wa Najeriya da Dala miliyan $52.88.
- An gurfanar da tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani Alison-Madueke a Birtaniya
- Alison Madueke na neman kotu ta hana Diezani amfani da sunansa
“A baya an sallama wa Amurka kuɗaɗen a ƙarƙashin shirin Yaki da kuma Ƙwato Kuɗaɗen Sata na Ma’aikatar Shari’ar Amurka.”
Ta ce hakan ya ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu wajen yaƙi da almundahana da kuma ƙwace dukiyoyin haram.
Ta ce kuɗaɗen da kadarorin da aka kwato bayan shari’ar da aka kammala a shakarar 2023 sun haɗa da gidaje da wasu kadarori a jihohin New York da California.