Gwamnatin Amurka ta yaba da kokarin da kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu ke yi wajen tsaurara tsaro a kasashen biyu.
Hakan na zuwa ne bayan wani kashedin da Amurkan ta yi na yiwuwar afka wa Abuja, Fadar Gwamnatin Najeriya da hare-haren ta’addanci da ma wasu wurare da ke wajen birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.
A sanarwar da Ma’aikatar Kula da Hakokin Kasashen Wajen Amurkan ta fitar, ta yaba wa kokarin da Najeriya da Afirka ta Kudun ke yi a bangaren tsaurara tsaro da nufin tunkarar duk wani hari da ya doshi manyan birnanen kasashen biyu da Amurkar ta ce ta hango.
A ranar Alhamis da ta gabata ne dai Amurkar ta yi kiran ma’aikatan jakadancinta da ke Abuja da su fice daga Najeriya, kwana guda bayan ta yi hakan ga su ma ’ya’yanta da ke a Afirka ta Kudu.
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu, ya nuna rashin jin dadi ganin yadda Amurkar ta yi gaban kanta wajen bayyana hadarin ba tare da ta tuntubi gwamnatin kasar ba.
An tsauraro a Najeriya
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce ta kara tsaurara tsaro a fadin kasar daidai lokacin da Amirka ta umurci ma’aikatan jakadancinta da zamansu bai zama dole a kasar ba su fice daga Abuja bisa yiwuwar kai hare-hare.
Duk da cewa babu wani cikakken bayani kan gargadin da ofisoshin jakadancin wasu manyan kasashen duniya suka yi kan yiwuwar kai hare-hare, amma hakan ya sa jama’a da dama a birnin Abuja sun shiga zullumi.
Sai dai a cikin wata sanarwa da rundunar ’yan sandan kasar ta fitar ta ce ta umurci manyan jami’anta da ke fadin kasar da su kara kaimi wajen samar da tsaro musamman a birnin Abuja.