Amurka ta sanya takunkumin shiga kasarta ga wasu mutanen da ta ce sun yi magudi a zaben watan Nuwamban 2109 a Jihohin Kogi da Bayelsa.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce haramcin shiga kasar ya kuma shafi wasu mutane da suka aikaita ba daidai ba gabanin zabukan Jihar Edo da ke tafe a watan Satumba da kuma na Ondo da za a yi a watan Oktoban 2020.
- Saudiyya za ta bude zirga-zirgar jirage ranar Talata
- ‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro biyu, sun sace 10
- Mun kashe N4.27bn kan harkar tsaro —Gwamnatin Katsina
Pompeo ya ce duk da cewa ba a kai ga gudanar da zabukan na Edo da Ondo ba, kasarsa za ta sa wa mutanen takunkumi ne saboda wasu abubuwan da suka aikata.
Sanarwar da Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Morgan Ortagus, ya fitar ranar Litinin ta ce “A watan Yulin 2019 mun sanar da sanya takunkumi ga wasu ‘yan Najeriya da suka yi zagon kasa ga zaben watannin Fabrairu da Maris na 2019.
“Yau Sakataren Harkokin Kasashe Waje ya kara sanya takunkumin bayar da biza ga mutanen da suka yi zagon kasa ga zaben watan Nuwamban 2019 a Jihohin Kogi da Bayelsa da kuma na Jihar Edo da ke tafe a watan Satumba, sai na Ondo da za a yi a watan Oktoba.
“Wadannan mutane sun yi yadda suka ga dama wurin yin kutungwila ga dimokuradiyyar Najeriya ba tare da damuwa da ‘ya kasar ba”, inji sanarwar.
Sai dai sanarwar wadda ake ganin na cikin matakan Amurka na karkafa dimokuradiyya a Najeriya ba ta bayyana sunayen mutanen da haramcin ya shafa fa.