More Podcasts
Tun bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe Zaɓen Gwamna da aka gudanar a Jihar Ondo ranar 16 ga watan Nuwamba, hankula suka karkata zuwa ga ƙalubalen da ke gabansa.
Kama daga rikicin cikin gida a jam’iyyarsa ta APC zuwa ga barazanar jam’iyyun adawa da muradun al’ummar da ya yi wa alƙawura, anya Aiyedatiwa bai sha ta fi cikinsa ba kuwa?
- NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.
- DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci
Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari a kan abubuwan da Zaɓaɓɓen Gwamnan na Jihar Ondo ka iya fuskanta bayan ya sha rantsuwar kama aiki.
Domin sauke shirin, latsa nan