Kasar Amurka ta jingine yunkurin neman canjin gwamnati da take yi a kasar Syria, amma ta ce ba za ta bayar da kowane irin tallafi ba wajen sake gina kasar har sai gwamnatin Shugaba Assad ta canza salo.
Wakilin Amurka na musamman a Syria James Jeffrey ya ce dole ne Shugaba Assad ya sassauta ra’ayi domin kuwa har yanzu bai yi nasara a yakin basasar kasar da aka shafe shekara 7 ana fafatawa ba kuma har yanzu akwai ’yan tawaye kusan dubu 100 da ke filin daga.
Wakilin ya bayyana haka ne a wajen wani taron kara wa juna sani a birnin Washington, inda ya ce, “Muna kokarin mu ga sabon salo ne wurin tafiyar gwamnatin ba wai canjin gwamnati ba.”
An dai yi kiyasin cewa Syria za ta bukaci Dalar Amurka miliyan 300 zuwa 400 domin sake gina kasar. Amma Jeffrey ya yi gargadin cewa gwamnatocin kasashen Turai da cibiyoyin harkokin kudi na duniya ba za su bayar da tallafin komai ba matukar ba a samu wannan canji ba.
Ya ce “Kasashen Turai a shirye suke su taimaka amma fa sai Assad ya tabbatar musu da cewa a shirye yake ya sauya salon mulki kuma kasar ba za ta ci gaba da muzguna wa ’yan kasarta ba.”
A baya dai tsohon Shugaban Amurka Barrack Obama ya sha kiran a tunkudar da gwamnatin Assad amma daga baya ya mayar da hankali ne kan dakile ayyukan kungiyar ’yan ta’adda ta Daular Musulunci (IS).
A hannu guda kuma Shugaba Trump ya amince cewa akwai yiyuwar Assad ya ci gaba da mulki duk da cewa abin ba lallai ne ya yi wa wadansu dadi ba. Shi kuwa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo cewa ya yi Amurka ba za ta taimaki Syria da ko kwabo ba in dai Iran ta ci gaba da saka baki a rikicin.
Amurka ta yi kira ga Iran ta janye sojojinta daga kasar Syria wadanda tuni kasar Isra’ila ta yi Allah wadai da su, amma kuma ta amince cewa Iran din za ta iya shiga tsakani domin yin sulhu.
Jeffrey ya ce, “Ba lallai ne Amurka ta kulla kawance da wani bangare ba a rikicin Syria a nan kusa, amma kuma idan hakan zai faru muna son wanda kungiyar Tarayyar Turai za ta amince da shi idan da kasashen Larabawa na da damar shiga kungiyar.”