✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amurka ta haramta sayar da kayan China a kasarta saboda cin zarafin Musulmin Uighur

Amurka ta dauki matakin ne saboda yadda China ke cin zarafin Musulmin Uighur.

Shugaban Amurka, Joe Biden ya sanya hannu a kan wata doka da ta haramta sayar da kayan da aka sarrafa a yankin Xianjiang na China saboda yadda kasar ke ci gaba da musguna wa Musulmi ’yan kabilar Uighur a kasarta.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka ke dada tsami tsakanin kasashen guda biyu.

Sabuwar dokar dai Majalisar Dokokin kasar ce ta amince da ita a farkon wannan watan kuma za ta bukaci dukkan wanda zai shigar da kayan da aka sarrafa a yankin ya nuna shaidar da ke tabbatar da ba a yi amfani da karfinmutane wajen sarrafa su ba.

Yankin na Xinjiang dai ya yi fice wajen sarrafa auduga da na’urorin samar da lantarki daga hasken rana.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi kiyasin cewa akwai sama da mutum miliyan daya, yawancinsu Musulmi marasa rinjaye da aka daure a gidajen kaso daban-daban na yankin.

Amurka da sauran masu kare hakkin dan Adam dai sun bayyana matakin a matsayin kisan kiyashi.

Dokar dai ta tanadi tsattsauran hukunci ga duk wanda aka samu da hannu wajen karyata.

Sai dai matakin zai haifar da babban gibi ga kamfanonin kasar da suka dogara wajen samo kayan sarrafawa a masana’antunsu daga yan kin na Xianjinag na China

Ko a makon da ya gabata dai sai da wata kotu a Birtaniya ta yanke hukuncin cewa abin da China ke yi wa ’yan Uighur din ya fi kama da kisan kiyashi da kuma laifi kan dan Adam.