Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergey Lavrov, ya ce kasar Amurka da Rundunar Kawancen Tsaro ta NATO sun fi kowa amfana da rikicin kasar Ukraine.
Ya kuma yi zargin cewa Amurkan da NATO na son ganin bayan Rasha ta hanyar fakewa da rikicin na Ukraine.
- Hukuncin Rataya: Za Mu Daukaka Kara —Daliban Abduljabbar
- Sana’armu na cikin tsaka mai wuya —Masassaka turmi
A wata tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Rasha (TASS), Segey Lavrov ya ce, “Ayyukan kasashen Yamma baki daya da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, wanda shi ke kokarin aiwatar da bukatar tasu, ya tabbatar da ainihin manufar yakin na Ukraine.
“A bayyane yake cewa babbar manufar Amurka da NATO ita ce ta samun galaba a kan Rasha a fagen daga, ta yadda za su raunana ta, ko ma su ga bayanta gaba daya.”
Ministan a kan haka, ya tsaya kai da fata cewa Amurka ce babbar kanwa uwar gami a rikicin, kuma ta fi kowa amfana da shi.
Ya kuma ce Amurka na son yin amfani da yakin don canza dadaddiyar alakar da ke tsakanin Rasha da kasashen Turai, domin ta ci gaba da danne Turawan.
“Amurka na yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta rura wutar rikicin nan da neman ganin ya tsawaita. Hukumar Tsaron Amurka ta PENTAGON na yunkuri a fili na ganin cewa ta ci gaba da tunkudo kudade saboda yakin ya ci gaba, kuma suna bukatae sauran kasashen da ke takun saka da Rasha su ma su bi sahu,” inji Sergey Lavrov.