Majalisar Dokokin Amurka ta hana sayar wa Najeriya makamai da kuma jiragen yaki 12 na Dala miliyan 875 da Najeriyar ta yi oda domin yakar ayyukan ta’addanci.
Kwamitin Harkokin Wajen Majalisar Dattawan sun bukaci Amurka ta dakata da cinikin da aka kulla na sayar wa Najeriya jiragen yaki 12, kirar Cobra AH-1 ne bayan isowar wasu jiragen yaki samfurin Tucano guda shida da Najeriyar ta yi oda tun da farko.
Baya ga sayar wa Najeriya jiragen yaki guda 12 masu saukar ungulu, cinikin da aka dakatar ya hada da sayen injinan jirgi guda 28 kirar kamfanin GE Aviation da kuma na’urorin bibiyar jiragen yaki 14 kirar kamfanin Honeywell, da rokokin zamani guda 2,000.
Kwamitin Majalisar kan harkokin wajen Amurka ya hana sayar da jiragen yaki da makaman ne saboda damuwa kan abin da ya kira tauye hakkin dan Adam a yaki da ta’addanci.
Majalisar ta kuma bukaci gwamantin Shugaba Joe Biden ta sake nazarin alakar da ke tsakanin Amurka da Najeriya.
Wasu daga cikin ’yan Majalisar na zargin mulkin Shugaba Buhari ya fara rikidewa zuwa na kama-karya duk da matsalolin tsaro da kasar ke fama da su.
Batun sayar wa Najeriya makaman da sauran kayan yakin ya haifar da mahawara a majalisar a lokacin ta take tattaunawa kan matsalolin tsaro a Najeriya da kuma kare hakkin bil Adama a yayin yaki da ta’addanci.
Majalisar ta ce ta shiga tsaka-mai-wuya tsakanin taimaka wa Najeriya wurin yaki da ta’addanci da kuma matsalar keta hakkin dan Adam.
Sun bayyana rufe Twitter da aka yi a Najeriya da kuma kashe wasu masu zanga-zangar EndSARS a matsayin wasu daga cikin dalilan dakatar da cinikin.