Gwamnatin Amurka ta cire duk karin kudin da ta wajabta wa ’yan Najeriya su biya yayin neman kowace nau’in bizar zuwa Amurka.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Ferdinand Nwonye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ta zare ’yan Najeriya daga biyan kadin kudin neman bizar wadda ta ce an fara aiki da ita daga ranar 3 ga watan Dasumban da ya gabata.
- APC ta lashe zaben cike gurbin dan Majalisar Dokoki a Bauchi
- Wani mutum ya kashe makwabcinsa a jihar Osun
- Trump ya umarci a janye dakarun Amurka daga Somaliya
Ya ce wannan ci gaba na zuwa ne biyo bayan hukuncin da Gwamnatin Najeriya ta yanke a kan ’yan Amuka masu neman shiga Najeriya na cire musu duk wasu tsarabe-tsaraben neman bizar shiga kasarta.
A cewar Nwonye, “ana shawartar ’yan Najeriya da ke neman bizar shiga Amurka da su ziyarci shafin www.travel.state.gov domin samun karin haske.”
Ana iya tuna cewa tun a watan Agustan 2019 ne Gwamnatin Amurka ta sanar da karin kudin neman bizar shiga kasar a kan ‘yan Najeriya bayan Gwamnatin Najeriya ta kara wa ’yan Amurka kudin neman bizar shiga kasarta.
A wancan lokaci, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce, ’yan Najeriya da aka amince da bizarsu ta shiga Amurka za su biya karin kudi daga dala 80 zuwa 110 – kwatankwacin N28,800 zuwa N39,600.
A cewar Ma’aikatar, an kara kudin bizar ne bayan an kwashe watanni 18 ana tattauna wa da Gwamnatin Najeriya don ta yi wa Amurkawa rangwami daidai gwargwado amma abin ya faskara.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan Najeriyar da suka samu bizar Amurka bayan tsawwala farashi, su kan biya karin kusan dala 80 zuwa 110 – kwatankwacin naira N28,800 zuwa N39,600.
Yanzu Najeriya ta rage kudin neman bizar kan Amurkawa, inda yake kamawa daga dala 180 zuwa 150.