kasar Amurka da mafi yawan kasashen Tarayyar Turai na barazanar kakaba wa kasasha takunkumi. Saboda mamayar yankin Crimea da ke kasar Ukraine da ta yi, inda amurka ta doge kan cewa Rasha ta saba wa dokar duniya, ita kuwa Rasha ta ce, an yi w akundin tsarin mulkim Ukraine juyin mulki.
Wannan rikici na kasar Ukraine da Rasha, shi ke daukar hankalin duniya, domin manyan kasashen duniya sun nuna matsayinsu a kan rikicin. Uwa-uba kan al’ummar kasar ya rabu biyu, ibnda ake da masu goyon bayan Rasha da masu goyon bayamn Tarayyar Turai, wadanda suka shirya zanga-zangar “Euromaid,” har aka kori tsohon shugaban kasar daga mulki. Kuma masu mulkin kasar a halin yanzu ba su da cikakken karfin uiko a yankin Gabashi da Kudancin Ukraine, musamman Crimea, inda sojojin Rasha suka kutsa kai, inda ta tara sojoji har dubu shida.
Firayiministan Ukraine ya roki kasashenTurai su ba shi tallafin jagorancin siyasa da bunkasa tattalin arziki, inda ya ce har yanzu Crimea wani bangare ne na kasarsa. Amurka da gwamnatocin tarayyar Turai na ta neman mafita, don hana kasar Rasha mamaye kasar.
Wutar rikici ta fara ruruwa ne a tsakanin Ukraine da Mosko, bayan da masu zanga-zangar neman kulla alaka da Tarayyar Turai, suka kawar da gwamnatinsa, inda a kalla mutum 80 suka mutu a wani dandali da ke tsakiyar kasar. Ya ce har yanzu shi ne shugaban kasa. Kuma tun daga wancan lokaci sojojin da kasar Ukraine ta ce sojojin Rasha ne suka kutsa kai cikin Crimea, suka rika sintitiri a filayen jirgin sama, inda suka lalata na’urorin da ke filin, sannan suka mamaye wurin adana makaman suojojin kasar.
Yayin da Yammacin Ukraine ke bukatar kulla alaka da kasashe 28 na Tarayyar Turai, su kuwa al’ummar yankunan da ke Kudancin kasar, musamman Crimea sun fi kulla alaka da kasar Rasha.kasar Rasha tad ade tana son kwace zirin ruwan crimea, wanda a ada wani yanki ne na kasarta, kafin a yanke shi ya koma cikin kasar Ukraine a shekarar 1954. Don haka kasar Rasha ke biyan haraji ga gwamantin Ukraine, saboda amfani da tashar jirgin ruwanta da ke kusa da “Bakin teku – Black Sea,” da Sebastopol. Kuma kimanin kashi 60 cikin 100 na al’ummar Crimean sun dauki kansu a amtsayin ’yan Rasha.
Shugaban Tarayyar turai, Jose Manuel Barroso, a Larabar da ta wuce, ya bayar da sanarwar bai wa kasar Ukraine tallafin Yuro biliyan 11, wanda za a rika bayarwa tsilkli-tsilli na tsawon wkasu shekaru.
“Wannan tallafi ne na agaza wa kasar ta aiwatar da garambawul a harkokin gwamnati,” inji Mista Bosso.
Ya ce zai tattauna kan wannan tallafi a taron da kungiyarsa ta EU, inda ake sa ran halartar Sabon Firayiministan Ukraine, Arsenik Yatsenyuk. Za kuma su tattauna kan yiwuwar amfani da matakin soja don mayar da martini ga Rasha a mamayar da ta yi wa yankin Crimea.
Sojojin Rasha sun kwace ma’ajiyar makaman Ukrain masu cin dogon zango, kamar yadda Ma’aikatar tsaro ta kasar ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Wasu sojojin Rasha 20, tare da goyon bayan masoyansu na yankin, sun yi yunkurin mamaye sansanin Ebpatoria, inda aka so a kara, amma dai ba a yi harbi ko daya ba.