Ina so in san nau’o’in ciwon kai. Sa’annan idan ka ji wani bangare na kanka na ciwo ko da irin matsalar da hakan ke nufi?
Akwai ciwon kai nau’i-nau’i; wasu daga gundarin kai ko kwakwalwa suke faruwa wasu kuma ciwon wasu sassan jiki ke kawo su kamar zazzabi, wasu gadonsu ake yi, wasu kuma ciye-ciye da shaye-shaye da yawan aiki da gajiyar yau da kullum ce ke kawo su. Wasu suna da hadari wasu kuma ba su da shi.
Ciwon kai daga gundarin kai ya hada da ciwon barin kai daya (migraine), sai na goshi (tension headache), sai na saman hanci (sinus headache), sai na keya wanda hawan jini ya fi kawowa.
Shi na goshi da ake kira damuwa (tension) ko gajiya (stress headache) shi ne ciwon kai da ya fi kowane ciwon kai. Wato mutane da dama suna samunsa fiye da kowane irin ciwon kai, kuma yawan gajiya da aiki ba hutawa da damuwa ne ke kawo shi. A wasu lokuta ba goshi kadai yake rikewa ba, duk kan akan ji ya rike ya daure kamar rawani. Sai dai shi magunguna irin su panadol suna iya sa mutum ya ji dan sauki. Yana daga cikin ciwon kai wanda ba ya barin mutum har sai mutum ya canja yanayin abin da ke kawo masa damuwar.
Ciwon kai na bari daya da muke kira migraine shi ne wanda yake kama dama ko hagu, ana ganin kamar yana cikin wadanda akan yi gado, kuma mata sun fi maza yin sa. Don haka idan mutum na da ciwon ba a sa ran zai rabu da shi gaba daya, kamar dai farfadiya ko ciwon suga ko na hawan jini, sai dai ya zo ya tafi, ya zo ya tafi. Don haka mai irin wannan sai dai ya rika zuwa wurin likitan kwakwalwa ana rubuta masa magunguna masu karfi da za su rika kiyaye tashin ciwon da kuma magance shi idan ya tashi, domin magunguna kanana irin su panadol ba sa masa.
Na saman hanci kuma shi ne wanda muke kira sinus headache wanda ke kama masu murar sinusitis.
A keya akan iya jin daurewa ko ciwo a masu ciwon hawan jini wadanda bai sauka ba, duk da cewa a mafi yawan lokuta masu ciwon hawan jini ba su samun wani ciwon kai.
Sauran nau’o’in ciwon kan duk daga wani sashi na jiki abin ke farawa, kamar na zazzabi, na karancin jini a jiki da sauransu.
Duk lokacin da raina ya baci ba na iya magana kuma zan wuni da ciwon kai. Ko wannan wata matsala ce?
Daga Zainab, Rigasa
Amsa: Yauwa to kin ga irin ciwon kan da aka yi bayani a sama ke nan, ciwon kai na damuwa (tension) ne yake samunki idan kika shiga damuwa da bacin rai. Ke nan maganinsa shi ne yawan kai zuciya nesa, idan kin fahimta. Wato a rika daukar abubuwa da sauki ba da zafi-zafi ba.
Na karanta jawabinka kan dalilin da ke sa likitoci ke yin rubutun da sauran mutane ba sa ganewa. Ni ina ga kamar saboda kada a rika shan su ne a matsayin kayan maye, shi ya sa suke rubutu ta yadda ma’aikatan lafiya ne kadai kan iya gane rubutun.
Daga Femi M. Neja
Amsa: A’a watakila ba ka gane tambayar da aka amsa ba ce. Tambayar ita ce ta cewa masu kyamis da pharmacy ba sa gane wasu rubutun likitoci. Ka ga kuwa ai rubutu ya baci idan har wadanda aka rubuta wa rubutun sun kasa karantawa.
Sa’annan kana nuni da cewa kamar wannan rubutu haka ya kamata a yi shi a bobboye. A’a ai ba abin boyo a nan tunda likita zai fada wa marar lafiya cewa za a ba shi magani kaza mai aiki kaza. Sa’annan idan za a ba wa marar lafiya maganin dole mai ba da magani ya yi masa bayanin yadda ya kamata ya yi amfani da shi. To ka ga babu batun boye-boye.
Ina da ciwon suga ina shan magani, amma fitsarina karuwa yake kuma ina kara kiba. Ina mafita?
Daga Al’amin Muhammad
Amsa: Mafita ita ce ka yi wa likitan asibitin da kake karbar maganin wannan bayani, domin watakila magungunan ba sa aiki sosai, ko ba ka shansu yadda ya kamata.
Ni kuma wani kululu ne ya fito min a bayan wuya ban san lokacin da ya fito ba domin ba ya mini ciwo. Shin ko akwai matsala?
Daga Aliyu Yabo, Sakkwato
Amsa: Eh, duk wani kululu da ya fito a jikin mutum koda ba ya zafi ko radadi matsala ce wadda sai likita ya duba ya tabbatar maka akasin haka sa’annan za ka kwantar da hankalinka, domin wasu kululan da kari da ciwon daji haka suke farawa ba wani radadi.
Hakorana ne ke mini ciwo nake so a cire, shi ne wasu suka ce mini idan aka cire na kusa da shi zai kamu ya cire. Ko shin da gaske ne maganar mutanen?
Daga Nura Sahabi Suleja
Amsa: A’a ba gaskiya ba ce, barinsa ne ma zai sa na kusa su kamu, ba cire shi ba. Kana da zabi ko a cike ko a cire. Cikewar ita ce a rarake wurin da ya yi ciwon ko rami a cike shi da simintin hakori, shi ke nan. Idan ma cirewar kake so duk daya ba wata illa sai dai watakila ka kasa tauna kashi da wurin.
Ko yaya na yanke da reza ko wani abu sai in ji jiri kamar zan fadi. Ko me ke kawo haka?
Daga Halima Dorayi
Amsa: In dai ba zubar da jini sosai ba yawanci dimuwa ce ke kawo jirin a ’yar yanka kadan sabanin jiri wanda yawan zubar jini ke jawowa. Domin ko yaya akwai wadanda ba sa son ganin jini da sun gani sai jiri ya rika kwasarsu ko a jikinsu ne ko ba a jikinsu ba.
Ko zan iya shafa man zaitun a jikina a kullum?
Daga Bashir M. Ikko
Amsa: Eh, za a iya shafawa.