✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi: Mene ne ciwon Maloho?

Ranar 21 ga watan Maris  na kowace shekara rana ce da hukumomin lafiya na duniya suka ware domin yin tuni kan ciwon maloho. Mene ne…

Ranar 21 ga watan Maris  na kowace shekara rana ce da hukumomin lafiya na duniya suka ware domin yin tuni kan ciwon maloho. Mene ne ciwon Maloho? Maloho yaro ne ko yarinya da aka haifa da wata larura a kwayoyin halitta da ke sa karancin tunani da nakasa a kwakwalwa, ta yadda masu larurar za su iya zama kamar gaulaye ko wawaye. Wato bangaren tunanin su masu wannan larura bai cika ba, kuma sukan samu wasu kamanni daban da na masu lafiya. Sauran misalan alamunta sun hada da wararriyar fuska da kankantacciyar haba da katon harshe da katon wuya da rashin kwarin jiki gaba daya. Wadansunsu ma suna iya kasa magana ko samun tangarda a magana kamar in’ina. Maza yawanci idan suka girma ko sun yi aure ba sa iya haihuwa, matan nasu ma kadan ne ke iya haihuwa.

Ba gadon ciwon ake ba, domin iyayen wadannan yara idan aka auna kwayoyin halittunsu ba a ganin komai na tangarda, kawai dai rashin sa’a ake yi a haifi Maloho. Amma dai bincike ya nuna cewa matan da suka dauki juna biyu bayan kuruciyarsu, wato dab da tsayawar al’adarsu sun fi samun ’ya’ya Maloho. Don haka ne ma aka fi ganin ciwon a kasashen Yamma inda mata ba su cika haihuwa da wuri ba. Wato matsalar ta fi yawa a kasashen Turai da Amurka. A can a duk haihuwa 1000 sai an ga akalla daya mai ciwon Maloho. Amma a irin kasashenmu ma ana samu jefi-jefi.

Saboda girman wannan matsala ga masu ita da ma iyayensu a wadancan kasashe, zamani ya zo cewa suna iya kiyaye haifar yara masu ciwon Maloho. A yanzu a can ana iya yi wa mace mai juna biyu gwajin kwayoyin halittu a dan tayin tun yana ciki a gano mata ko yana da ciwon Maloho ko babu. Wannan suna yi ne domin a ba matar zabi idan an ga ciwon, ko ta yarda a cire ko a bar shi. Da yawansu sukan yarda a cire idan an gano birbishin ciwon a wannan gaba saboda kada su haifi Maloho.  

Duk da haka su wadannan masu ciwon Maloho sukan iya rayuwa su iya koyon abubuwa da dama, domin kusan sukan iya zuwa makaranta yawanci iya ta sakandare, kuma sukan iya samun aiki daidai da kwazonsu. A irin kasashen da suka fi yawa, wato kasashen Yamma doka ta tanadi a ware wasu guraben aiki domin irin wadannan mutane masu ciwon Maloho da ma masu sauran cututtukan nakasa, sabanin yadda dokokin daukar aiki suke a irin kasashenmu.