✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban(10

Ina fama da rugugin ciki. Ko me ke kawo hakan? Ya kuma zan yi na kiyaye aukuwarsa?Amsa: Rugugin ciki iri-iri ne, akwai wanda kan faru…

Ina fama da rugugin ciki. Ko me ke kawo hakan? Ya kuma zan yi na kiyaye aukuwarsa?
Amsa: Rugugin ciki iri-iri ne, akwai wanda kan faru yau da kullum ba tare  da wata matsala ba, kawai mutum na zaune shiru, sai ya ji cikinsa ko ‘yan hanjinsa na kara, wasu a hankali, na wasu kuma da karfi har ma na kusa da shi su ji, su dauka ko tusa ce. A lokuta da dama kuma yunwa na iya kawo rugugin cikin wanda shima kararta ta bambanta daga wani zuwa wani. Akwai kuma nau’in karar ciki bayan cin wasu nau’uka na abinci kamar masu sa taruwar gas (kamar wake), ko masu tauri (kamar doya), wato masu karfi wanda sai hanji yayi da gaske yake narkasu.
Sai kuma na rashin lafiya, kamar toshewar hanji, ko nannadewar hanji wanda kan toshe gaba daya ko kuma ya dan toshe a wani bangare na dan wani lokaci, kafin ya saki; akwai kuma na olsar hanji, wato gyambon bangon hanji kamar yadda kan faru a bangon ciki. To su wadannan nau’i sun dan bambanta da sauran, tun da a nan rugugin yana zuwa da murdawar ciki mai zafi, wani lokaci ma da amai, ko kasa yin bayan gida na tsawon kwanaki, da yawan kumburin ciki.
To idan irin alamun can na farko mutum ke samu ba abin damuwa ba ne ba sai ya nemi wani magani ba, kawai sai dai watakil ya canza cimaka, ya lura da abin da ke kawo masa rugugin ya kiyayesu. Amma idan kashi na biyu ne mai sauran alamu kamar yadda muka fada, to ba zama dole sai mutum ya je an binciki lafiyar hanjin nasa.

Ni kuma idan na sha shayi ko koko mai zafi sai kirjina da cikina su rika mini zafi ko mene ne dalili?
Daga Jamila H. Lagos

Amsa: Wannan ma ya fi kama da alamun Olsa wato gyambon bangon ciki ko na farkon hanji. Sauran abubuwan da za su iya kawo hakan sun hada da ciwon zuciya musamman idan ke mai kiba ce sosai. Domin wani nau’i na bugun zuciya ko ciwon zuciya haka yake farawa ya rike kahon zuci ko kirji kamar olsa a lokacin da ake cin abinci, wato ya fi zuwa lokacin cin abinci ko lokacin motsa jiki. Don haka kema dai baki ga ta zama ba dole sai an binciki dalili, ba lafiya ba ce. A yi miki gwaje-gwaje da bincike na ciwon olsar da na ciwon zuciya duka shi ya fi kafin a ce ko wanne ne.

Wani lokaci idan na tashi da safe sai kafata ta fara ciwo har ta kai ba na iya takawa. Kuma zan ga ta dan kumbura, sai na sa ruwan zafi na gasata take sauki. To sai na je asibiti aka dauki jinina aka auna, likita ya ce kada na sake cin jan nama ya rubuta mini wani magani Zyloric ya ce na yi ta sha. To ina sha, amma ina jin ciwo har yanzu. Ina neman magani.
Daga Haruna B. Kaduna

Amsa: E, wadannan alamu ne na ciwon sanyin kashi. Amma da yake sanyin kashin iri-iri ne, shi ya sa likita ya baka gwajin jini ka je ka yi don ya gano ko wanne ne. Watakil kuma a gwajin jinin an gano ciwon sanyin kashi nau’in Gout ne ke addabarka. Shi irin wannan nau’in ciwon sanyin kashi na
Gout an fi samunsa ta gado, wato ya fi bin dangi, wato idan ka bibiya akwai mai irinsa a ‘yan uwanka na kusa. Wanda bai da mai irinsa a danginsa da wuya ya yi. Wadansu sinadaren Acid na abinci ne maimakon koda ta fitsarar da su, sai su rika taruwa a gabobi kamar gwiwowi da idon sawu da karshen ‘yan yatsu. Sun ma fi taruwa a babban yatsa din fiye da ko’ina. Su wadannan sinadarai na Uric Acid su suke kawo wannan zogi da kumburi.
Wata hanyar tabbatarwa da ciwon shi ne na diban ruwan wurin kumburin a auna a ga sinadaran a kan madubin binciken likita wato Microscope.
Wadannan magunguna da aka baka basa rage zogin sai dai su rage taruwar sinadaran a jiki. Don haka watakila sai ka koma an baka masu kashe zogi sa’annan abin zai lafa. Kuma haka ne cewa dole ka rage cin jan nama da ma sauran abinci masu sa taruwar wannan sinadari irinsu alaiyahu, da ruwan barasa. Akwai a sauran nama irinsu kaza da kifi amma ba su kai na jan nama ba.
Daga nan dabarar gashi da ruwan zafi ko daga kafar sama, duk ba sa yi wa masu irin wannan matsala wani alfanu, wato irinku masu ciwon sanyin kashi. Masu buguwa ne kamar targade da dan gociyar kashi ko ta wurin guntsi irin na ‘yan wasa ruwan dimi ke wa amfani. Suma bincike ya nuna idan sabon buguwa ne kankara ta fi amfani wajen rage zogi da kumburi a kan ruwan dimi, ruwan dimi ya fi yi wa buguwar da ta dan kwana biyu.

A yi mini karin haske mana dangane da ciwon kai da ke yawan addabata masaman  idan nasamu tsawon lokaci ban ci abinci ba, ko kuma idan na samu dogon zama a kujerar mota.
Daga Garba Sabiyola Gashua

Amsa: E, dama abinda ya fi kawo ciwon kai kenan wato yunwa da gajiya.
Sauran abubuwan da kan kawo ka ji ciwon kai sune shigar kwayoyin cuta jiki, kamar na mura, da na maleriya da na zazzabin tafot da sauransu, amma su wadannan akwai sauran alamu da zaka ji. Su na yunwa da gajiya saboda sikarin jininka ya yi kasa shi ne ke janyo yunwar da gajiya da ciwon kai. Watakil da ka ci abinci ka huta kuma kake jin komai ya dawo daidai. To in dai haka ne kada ka damu, ba wata matsala, amma in dai ko ka ci abinci ka huta ba ya sauki to kaima zama bai same ka ba.