✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban

Likita ni fari ne a da, amma yanzu duk na bi na yi baki. Ko me yake sa haka? Kuma mece ce mafita? Daga Aminu…

Likita ni fari ne a da, amma yanzu duk na bi na yi baki. Ko me yake sa haka? Kuma mece ce mafita?

Daga Aminu A.

Amsa: Ai ba kai kadai ba Mallam Aminu, kusan duk kanwar ja ce. Kusan ko wane jariri idan aka haife shi za ka ga da haskensa, ko ma fari kal, amma da ya fara girma ya kai shekaru biyar zuwa goma zai dafe. Amma an ce kusan kowa, don haka ba kowa ba, sai wanda rayuwa ta dan yi wa wahala ko kuma wanda dama a kananan halittunsa na gado ya gaji duhun fata sosai. Wato ke nan idan aka haifi yaro kal, kuma ya girma a gidan jin dadi da rashin wahala ko a kasar da ba rana sosai kamar nahiyar Turai, zai wuya ya rikide.

Kusan ke nan dai za a iya cewa yanayin muhalli da wahalar rayuwa da wasu kan fuskanta ko a gidansu ko a makaranta (wasu da dama a shekarun karatu) ke dafar da su. Tun daga shiga rana, rashin isasshen hutu da rashin isasshen abinci nau’in protein mai gina fata da kara mata kyau, duk wadannan yau da kullum wasu sai sun fuskance su. To ka ji dalilan. Za ka ga watakila mata ba su cika samun matsalar ba, saboda mata ba su kai namiji shan wahalar duniya ba, kuma su jikinsu na samar da sinadarai masu gyara fata, sa’annan duk da haka kuma sun fi namiji dama da ikon samun kayan gyara fata, tun daga na ciye-ciye har na shafe-shafe..

Mafita ke nan ita ce a daina shiga rana (idan zai yiwu), da samun kwanciyar hankali da yawan hutu, da samun cimaka ta abinci mai gina jiki na protein a kullum da wanka da sabulai da shafa mayuka masu kare fata daga rana gangariya, ba na bilicin ba.

 

Me ke kawo yawan ciwon kai, ba mai tsanani ba,mai yawo daga wannan gefen zuwa wancan, kuma sai da safe idan an tashi daga barci ya fi yi.

Daga Lawal Muhammad, Jigawa

Amsa: Wannan yana kama da irin ciwon kai da kan faru idan kwayoyin cuta irin na su zazzabin typhoid ko na maleriya suka shigi mutum. Amma kuma ba tabbas, tun da ban duba ka ba. Wato ke nan zai iya yiwuwa ma daga yawan shiga rana ne, ko hawan jini, ko matsalar idanu. Ga su nan abubuwan da kan jawo ciwon kai birjik. Idan ka samu likita ya duba ka kuma ya yi maka aune-aune da gwaje-gwaje zai iya gano takamammai inda matsalar take.

 

 Me ke kawo kaikayin ido? Domin ni idanuna na yawan kaikayi.

Daga Hassan Sadi

Amsa: Akwai abubuwa da dama da kan iya kawo kaikayin ido, tun daga yawan shiga rana, zuwa kura, zuwa shigar kwayoyin cuta zuwa borin jini da sauransu. Yana da kyau ka ga likitan ido ya gano maka ko mene ne, musamman ma idan idanun na yin ja yayin kaikayin.

 

Me ke kawo borin jini? Wani na iya dauka daga wani kamar ta hanyar yin amfani da soson wanka?

Daga Maman Haidar

Amsa: Borin jini wasu kwayoyin jini ne ke kawosu. Kwayoyin da akan kira white blood cells, sune suke sakin sinadarai masu suna histamine sai a samu borin jini, wanda alamunsa kan nuna kamar kaikayin jiki, ko jiki ya yi birdin-birdin kamar kuraje haka. A ciki kuma ya sa gudawa da kumburin ciki.

Ba a daukar borin jini daga wani zuwa wani, kamar yadda ake daukar kwayoyin cuta, amma ana iya gadon matsalar daga iyaye. Idan mutum yana yawan samun borin jini sakamakon wani bakon abu da ya shiga jikinsa, to ‘ya’yansa ma za su iya yawan yin borin jini.

 

Me ke sa wa idan na kwanta barci sai kafafuwa na su kumbure, tafin na mini kaikayi. Wani lokaci har hannuwana ke sankarewa. Ko wace matsala ce hakan?

Daga Alh. Musa Lagos

Amsa: Akwai cutukan jiki da dama masu saka irin wadannan alamu amma dai zai fi kyau kada a lissafosu don kada a baka tsoro. Ko ma dai mene ne ba lafiya bane mutum ya rika samun kumburin kafa da hannu da sankarewarsu. Don haka baka ga ta zama ba Alhaji Musa, sai an binciki lafiyarka za a gano mene ne.

 

Na kan yi fama da karancin barci, kuma idan hakan ya yi yawa yana sa mini ciwon jiki kamar mai zazzabi kamar maras lafiya. Ina mafita?

Daga Adamu Madaci, Rano

Amsa: To ka ga kai ba za a ce kai tsaye sai likita ya duba ka ba tukuna. Shawara za a baka cewa ka guji abubuwan da ke hana barci. Idan kana shan sigari ko kana yawan cin goro, ko kai ma’abocin shayi ne ko coffee ko kana tu’ammali da wasu kwayoyi, to sai ka ajiye, (ko kuma a ce ka fara ragewa, domin ajiyesu farat daya ma matsala zai jawo). Idan kana amfani da ko da daya daga cikin wadannan, zai iya sa maka duk alamun da ka zayyano. Idan ba ka yawan amfani da ko da daya daga cikin wadannan da aka lissafa to sai ka ga likita.

 

Wai shi maganin tramal ainihinsa maganin mene ne? Ina gaskiyar cewa yana sanya maye idan aka sha?

Daga Dantaki, Bauchi

Amsa: Shi ainihin tramal magani ne na ciwon jiki da zazzabi. Idan aka sha shi daidai yadda aka tsara shansa, wato yadda likita ya rubuta ba za a yi maye ba, kuma kwakwalwa ba za ta rikice ba ta sa mutum ya ji idan bai sha ba baya jin dadin jikinsa.