Na karanta bayaninka a kan kariya daga ciwon zaizayewar kashi. Tambayata ita ce mene ne sunan ciwon a harshen Ingilishi?
Amsa: Sunan ciwon a likitance shi ne osteoporosis. Kalmar harshen Latin ce ba Ingilishi ba, kalmomi ne guda biyu wato osteo wanda ke nufin kashi da porosis wanda ke nufin rarakewa ko zaizayewa, aka hade. Idan za a yi karin bayani game da harshen likitanci, kada masu karatu su dauka daga turancin Ingilishi likitanci ke samun kalmominsa, a’a daga turancin Latin ne na kasashen Girkawa da Rumawan zamanin da aka samo mafi yawa daga kalmomin likitanci. Turawan Girka su ma sun samo da dama daga kasashen Gabas kamar daga kasar China da kasashen Larabawa.
Wato kusan shi turancin Ingilishi shi ma yana da kalmominsa na cututtuka daban da na Latin, kamar yadda Hausa ma take da su. Misali kalmar makero ta Hausa da Ingilishi ringworm ne da Latin kuma wanda akan koyar a littafin likitanci shi ne Tinea Capitis, haka da sauransu.
Idan na sha abu mai zaki kamar rake, bayan wani dan lokaci sai bakina ya rika tsami. Ko hakan matsala ce, kuma mene ne abin yi?
Daga Sa’idu Adamu, Potiskum
Amsa: A’a ba wata matsala ce babba ba, kwayoyin cuta ne suke mai da sukari zuwa sinadarin acid mai tsami. Don haka yawan kurkure baki bayan shan abu mai zaki da yawan aswaki zai rage wannan.
Mutum mai cin abinci yana yawan shan ruwa hakan zai iya samar masa da katon ciki?
Daga Bashiru Musa Kura
Amsa: A’a sai dai akasin haka, wato sai dai ma ya rage, tunda ai katon cikin na teba ne, kuma daga abinci ne, amma idan ana yawan shan ruwa yana nufin abinci ya ragu, teba ma sai ta ragu.
Mene ne alakar ciwon kirji da cin gyada ko gasasshiyar masara? Domin ni idan na ci su sai in ji zafi a kirjina
Daga Hassana A., Kaduna
Amsa: Ba wata alaka a likitance da aka sani da cin masara kan sa ciwon kirji. Watakila sai dai ko gyada, tunda wadansu suna samun borin jini idan suka ci ta, wanda zai iya sa kullewar ciki. Sai dai ko idan da ma can kina da ciwon olsa ko na zuciya wanda za ki iya zuwa a duba a tantance
Me ke sa mutum ya ji cikinsa ya kulle idan ya ci abinci?
Daga Sadik Abdullahi Bichi
Amsa: Abubuwa da dama, kamar yadda muka sha fada, don haka sai an duba mutum idan yana yawan samun irin wannan.
Me ke sa tari tare da jini?
Daga Abdulhamid Ahmed Bagiwa
Amsa: Ko ciwon numoniya wato danshin kirji, ko na TB, ko na daji da sauransu. Mai samun wannan sai shi ma ya je an duba shi.
Mene ne illar shan shisha?
Daga Yusuf M.K
Amsa: Ai ta ma fi sigari illa wato duk wasu illolin sigari da muka taba magana a kai, wato ita shisha ta ninka illolin sigari ninkin-ba-ninkin saboda ko a girmansu da abin da ake zukar za ka ga ba daya ba ne, shisha ta fi girma, hayakinta ya fi yawa.
Idan mutum na jin zafi a cikin kashinsa wane irin likita ka ce zai gani?
Daga Bashir Safiyanu, Kano
Amsa: Likitan cututtukan sanyin kashi wato Rhematologist za ka nema a babban asibiti. Idan ya duba ya ga ba nasa ba ne, misali idan matsalar ta likitan kashi ce, zai iya turaka can.
Me ke kawo wata irin mura da ba ta jin magani? Domin ni ciwona ke nan, na sha magunguna na ga likita an rubuta mini magunguna ba sauki. Ya ya za a yi?
Daga Umar Abaji Zamau
Amsa: Eh, akwai wata irin mura kusan kanwar ciwon asma ce wadda ba ta cika jin magani ba. sunanta chronic rhinitis. Idan ka samu ka ga likitan kunne da hanci wato ENT zai iya rubuta maka magani mai karfi wanda zai rika sa wa murar ta lafa, amma watakila ta rika tashi jefi-jefi.
Yawancin masu samun ciwon idanu sukan fara cewa suna ganin hazo-hazo. Ko me ke sa haka kuma mene ne magani?
Daga Musa Wali Samaru
Amsa: Eh, saboda ciwon idon da ya fi yawa a duniya mai kawo rashin gani alamarsa ita ce ta fara gani hazo-hazo, wannan ciwo kuwa shi ne ciwon hakiya. Maganinsa kuma shi ne tiyata.
Idan ina aiki ko zirga-zirga ina ganin jijiyo na fito mini amma idan na zauna wuri daya sai su koma. Ko hakan matsala ce?
Daga Khalil M.A
Amsa: A’a ba matsala ba ce
Me ya sa ba a iya shan ruwa irin wanda ake sa wa mutum ta jijiya?
Daga Salahuddeen A
Amsa: Ko za ka gwada ne Malam Salahu? Wadansu za a iya sha amma wadansu ba za a iya sha ba. Shi wannan ruwan ba a yi shi don ciki ba domin ko dai gishirin ciki ya yi wa ciki yawa ko kuma sukarin ciki ya yi yawa. Kuma ko a asibiti idan akwai yadda za a ba mutum magani ko ruwa a baki mun ma fi son haka fiye da ta jijiya. To amma a wasu lokuta dole sai ta jijiyar kai-tsaye domin ceton rai, kamar idan mutum ya suma ko ya dimauce da zafin ciwo ba zai iya shan wani abu ba.
Me ke kawo mutum ya kasance sam shi ba ya so ya shiga mutane? Ko kallonsa mutane suka yi sai ya ji ba ya jin dadi.
Daga Adamu A.
Amsa: Ciwo ne na tunani, mun taba bayaninsa a nan a baya. Wato wata tangarda ake samu a kwakwalwa takan sa wadansu mutane samun irin wannan. Idan mutum na fama da irin wannan sai ya tuntubi likitan kwakwalwa wanda zai yi tambayoyi ya tabbatar kafin ya zayyana maka mafita.
LAFIYAR MATA DA YARA: Amsoshin tambayoyi
Muna da wani yaro dan shekara hudu wanda har yanzu maganarsa ba ta fita sosai. Ko akwai matsala?
Daga Danliti A.
Amsa: Eh, akwai matsala, mun taba magana a kan wannan yallabai. Za ka iya fara sa shi a makaranta ka gani, bayan watanni idan ka ga babu ci gaba sai ka nemi asibitin kurame wadanda suke da speech therapist wato ma’aikacin lafiya mai koyar da magana (kamar akwai a asibitin kunne a Kaduna)
Mace mai ciwon dajin mahaifa ko mai ciwon sanyi za ta iya daukar juna biyu?
Daga MD Hidima Bentures
Amsa: Eh, dukkansu mata masu ciwon daji a mahaifa da masu ciwon sanyi wadanda ba su yi tsanani ba za su iya samun juna biyu, amma dai sai an tona, wato akan iya samu amma ba kasafai ba.
Da ina ganin al’adata duk wata amma yanzu wajen wata uku ke nan ban gani ba. Abin ya fara ba ni tsoro. Shin akwai matsala ke nan?
Daga R.B.D
Amsa: Ni ma abin ya ba ni tsoro. Daukewar al’ada har ta wata uku amma ba ki yi kokarin neman dalili ba?
Me ke sa fatar jaririna ba ta rabo da kuraje?
Daga Misis. B.Z. Kaura Namoda
Amsa: Eh, wadansu jariran haka fatarsu take ko don zafi ko zufa, ko watakila ruwan wanka da fitsarin da ya dade a jiki a cikin napkin. Za ki iya fara neman maganin kuraje na jarirai na sudocrem a kemis ki rika shafa masa ki gani, idan bai yi aiki ba sai kin dangana da likita
Sai amsar tambayar Mustapha Suleja Maje: Amsarka ita ce babu wata matsala idan ka yi hakan.
Shin yawan shan magungunan kashe zogin ciwon mara a al’ada zai iya yin wata illa?
Daga M.N.S
Amsa: A’a ba zai wa mara illa ba, amma za su iya yi wa bangon ciki illa, su sa olsa ko gyambon ciki.
Ni kuma ’yata ce wani kululu ya fito mata a kasan ciki. Ko akwai matsala?
Daga Nasir S. Gusau
Amsa: Eh, akwai matsala, yana da kyau likitan yara ko na tiyata ya duba kululun ya ba da shawarar me za a yi.
Wane magani ne mace za ta sha madadin allurar tazarar haihuwa?
Daga Muhammad Musa Sokoto
Amsa: Akwai magani a asibiti na sha na tazarar haihuwa, kuma shi kyauta ne ma. Ku je ku duba.
Shin akwai maganin da ke rage ko magance miyau a mace mai juna biyu?
Daga Rukayya H. Gombe
Amsa: Eh, akwai, idan kika je awo ki gaya wa likitar za ta rubuta miki. Yawancinsu sai dai su rage yawan miyan ba sa tsayarwa gaba daya.