✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban 02

Likita ko me ke kawo ciwon tautau ne?Amsa: A likitance idan aka ce tautau ana nufin wani ciwon fata na leishmaniasis da kwayar cutar leishmania…

Likita ko me ke kawo ciwon tautau ne?
Amsa: A likitance idan aka ce tautau ana nufin wani ciwon fata na leishmaniasis da kwayar cutar leishmania din ke kawowa. Amma da yake wannan ciwo ya ragu, an fi kiran makero da tautau tunda suna kamanni da juna. Tautau na ainihi ya fara dawowa sakamakon ciwon kanjamau.
kwayar cutar fungus ita ce ke kawo makero. Ciwo ne mai wuyar sha’ani, domin kusan sai an yi da gaske yake tafiya ko da an shafa magani. Ya fi kama yara wadanda suka fara zuwa makaranta ko wadanda suka fara fita wasa, domin kwaso shi ake a jikin wasu yaran a makaranta ko a wurin wasa. Akwai magani iri-iri kuma ba sai a asibiti ba, ko a kyamis za ka iya nema. Akwai kamar Whifield ointment, akwai miconazole da dai sauransu. Idan aka fada wa mai kyamis zai iya duba maka domin suna cikin magungunan da kowa zai iya saya (wato ober-the-counter medication) kamar irin su panadol da bitaman C. Idan aka shafa magani ya ki tafiya, to sai an je an karbi na sha, wanda su kuma sai likita ya rubuta a takardar asibiti.
Ko wadanne alamomi masu ciwon HIb suke ji a jikinsu?
Daga Sani, Garki da Maloli, Kano
Amsa:  Masu dauke da kwayar cutar HIb kusan ba sa jin komai a jikinsu sai cutar ta fara zama AIDS wato kanjamau. Wannan kuma yakan iya daukar shekaru tun daga biyu har goma sha wani abu dangane da karfin garkuwar jikin mutum. Mutum mai karfin garkuwar jiki zai iya kaiwa shekaru goma cutar ba ta zama kanjamau ba, maras karfin garkuwar jiki kuma cikin shekaru biyu ko uku da shigar kwayar cutar jiki alamu ke fara bayyana. Don haka da dama masu kwayar cutar ba su ma san suna da ita ba. Idan aka fara ganin yawan rama, ko yawan tari, ko yawan zazzabi ko yawan gudawa na fiye da tsawon wata guda duk da cewa an sha magani amma suka ki tafiya, to sai an binciki mutum a tantance ko alamun kanjamau ne.
Ko mene ne illar hada magungunan asibiti da na gargajiya domin sai na ji ana cewa zai iya kawo matsala.
Daga Zahradden Shifa
Amsa: E, kwarai kuwa, ko a na Turawan ma ai ba a hada wasu da wasu. Akwai wadanda idan aka hada su a lokaci guda za su iya kawo borin jini, ko wata matsala ga jikinka kamar lalata koda ko hanta, akwai wadanda daya zai iya rage wa daya karfi, da dai sauransu. To irin abin da ake tsoro ke nan idan aka ce maka kada ka hada maganin gida da na asiibiti, domin da yawa ba a san abin da zai je ya auku ba, idan wadannan sinadarai suka hadu a jiki.
Ko da gaske ne danyar madarar shanu za ta iya sa wasu cututtuka?
Daga Saifullahi, Badawa
Amsa: E, duk kwayar cutar da ke jikin wannan saniya za ta iya zuwa madararta. Wadanda aka fi sani a kasashenmu su ne kwayoyin tarin TB irin launin shanu, wadanda za a iya kwasa idan ba a yi hankali ba. Don haka an fi so a tafasa madarar shanu kafin a sha.
Ko da gaske ne aya za ta iya sa hawan jini?
Daga Ilham, Maiduguri
Amsa: A’a, sai dai ma ta rage, domin sinadarin fibre da ke jikin tukar yakan tsane maikon jikin hanji, wanda kowa ya san idan ya bi jiki zai iya kawo hawan jini.
Ni kuma ina ganin kumburin kafa musamman da zafi. Me ke kawo haka?
Daga Zangi, Hadejia
Amsa: Cutuka da dama, tun daga irin kumburin nan da ake kira tundurmi, ko ciwon koda ko na hanta ko na zuciya, duk za su iya zuwa da kumburin kafa. Amma dai da likita ya gani ya lallatsa, zai iya hasashen ko na mene ne. Sa’annan ya rubuta gwaji don a tabbatar.
Me ke kawo yawan faduwar gaba ne, sai na ji kamar ana daka? Sai kuma na ji kamar barci idan yana min, amma ko na kwanta ba barcin. Matsala ce?
Daga Maryam Fatakwal
Amsa: kwarai kuwa, ko dai zuciya ita kanta ke da matsala ko kuma makoko domin ciwon makoko yana saurin taba zuciya ya kawo irin wadannan alamu ko da bai kumbura ba. Wato dai zama bai same ki ba, don sai an yi gwaje-gwaje da aune-aune da hotuna an tantance.
Mene ne amfanin saka detol a cikin ruwan wanka ne ko na wanke baki?
Daga Mu’azu, Funtua
Amsa: Shi wannan sinadari yana da maganin kashe kwayoyin cuta ko kuma rage musu karfi a ruwa. Idan ruwan da kake wanka da shi ko kake wanke baki da shi, ba ka tabbatar da tsabtarsa ba, za ka iya diga masa wannan sinadari.
Me ke kawo fata ta rika tsattsagewa da zogi?
Daga Umma, Zage
Amsa: Abubuwan da suke kawo haka sun hada da yanayi, domin wasu sun fi ji lokacin hunturu. Sai yawan amfani da sabulai ko mayukan shafawa masu kyamikal irin na kodar da fata, sai rashin samun isasshen bitamin a abinci, musamman na rukunin E, wanda ake samu a man kifi da man zaitun. Akwai kuma wasu haka nan aka halicce su, matsalarsu ke nan fata kullum a bushe, a tsattsage. Irin wadannan za ka samu ba mutum daya ba ne kawai a gidan, wato akwai wani dan uwa a gidan ko na jini a nesa mai irin matsalar. To idan wannan ne dole mutum ya zama kullum cikin shafa mai, kamar basilin maras kamshi.
Me ke kawo mutum ya ji wani abu na yawo a jikinsa kamar kiyashi?
Daga Idris, Jibiya
Amsa: Abubuwan da kan kawo haka su ne abubuwan da kan taba lafiyar lakar jiki wato jijiyoyi. Abubuwan kuwa su ne yawan suga a jini kamar ciwon suga, yawan shan barasa, yawan kiba, rashin wasu sinadaran bitamin kamar na rukunin B6 da B12, wadanda ake samu a kayan marmari da na hatsi iri-iri.
Me ke kawo ciwon kai bari guda ne?
Daga Sa’adu, Funtua
Amsa: Abubuwan da kan kawo ciwon kai bari guda, a likitance, sun hada da wanda muke kira migraine, da cluster headache da tension headache, ko trigeminal neuralgia idan yana zuwa har tsagin fuska, ko ma hawan jini, ko ma wani abu daban a cikin kwakwalwa kamar tsuro, musamman idan ana gani dishi-dishi. Idan aka sha panadol ba sauki, sai mutum ya samu ya je a tantance ko mene ne, domin dukansu sukan bukaci magunguna masu karfi a mafi yawan lokuta.
Mutum ne yake yawan yin tunani da mantuwa, a wasu lokuta ma har da maganganu shi kadai. Ko mene ne abin yi?
Daga Angon Khadija
Amsa: Alamu ne masu kama da ciwon damuwa wato depression, ko wani ciwo madangancin wannan na kwakwalwa. Shawara a samu a ga likitan kwakwalwa.

 

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin Tambayoyi

Likita ko motsa jiki ga mata ta hanyar tsallen igiya (wato skipping) zai iya kawo wata illa?
Daga Bilkisu Kakaki
Amsa: A’a, ba wata matsala. Yana daya daga cikin motsa jikin da mata za su iya yi a gida. Matan da suke motsa jiki mai tsanani ne irin na maza, kamar kwallon kafa ko tsere sukan iya samun tsawon lokaci kafin su samu juna biyu idan suka yi aure, saboda al’adarsu takan iya daukewa lokutan da suke wannan motsa jiki mai tsanani.
Me ke kawo ciki ya yi ta kugi kodayaushe?
Daga Maman Zainab
Amsa: Akwai kugin ciki na yau da kullum; akwai mai nuni da matsala. Idan mutum na jin yunwa, cikinsa zai iya kugi, wannan ba matsala. Idan mutum ya ci abinci mai sa hanjinsa aikin wahala kamar wake, taura, goruba da ire-iren abinci masu tauri, ciki zai iya kugi, amma ba gudawa. Idan mutum ma ya ci abincin da ya fara lalacewa ko yake da kwayoyin cuta, ciki zai saki, ya yi ta kugi, sa’annan gudawa ta biyo baya. Idan kuma mutum cikinsa na kugi a kodayaushe, amma ba ciwo ba gudawa, shi ma ba matsala.
Likita ko me ke kawo kurajen gaba ne ga mata da maza? Kuma da gaske ne wani zai iya shafa wa wani?
Daga Rabi’u, Zaria.
Amsa: kwarai kuwa, kuraje a mace ko namiji za su iya nuni da ciwon sanyi wato ciwon da mace za ta iya dauka daga namiji ko akasin haka. Idan haka ta faru, sai an duba an ga irin kurajen domin kowanne da maganinsa, don wani zai iya zama daga kwayar bakteriya, wani kuma bairus, don haka masu cewa a rubuta musu magani, ba a tantance ba, sai su danne kunya su je asibiti. Kuma sai an ba abokin zama ko abokiyar zama da ma sauran matan mutumin dukansu ko nawa ne ko ba su da kurajen kafin matsalar ta bar gidan. Don haka mata da miji ne za su je, ba mace kadai ba, ko hakan zai maganin kunyar.
Watanni uku ban ga al’ada ba sai yanzu ta zo. Ko akwai matsala?
Daga Umma, Kano
Amsa: E, al’ada ko wata daya ta tsallake akwai dalili, ballantana wata uku. Ki samu ki ga likita, musamman ma idan ke matar aure ce.