✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban

Da gaske ne yawan cin gyada yana kawo kurajen fuska? Daga Nasiru Kainuwa, Hadejia Amsa: E, ga wanda yake da fuska mai saurin yin kuraje,…

Da gaske ne yawan cin gyada yana kawo kurajen fuska?

Daga Nasiru Kainuwa, Hadejia

Amsa: E, ga wanda yake da fuska mai saurin yin kuraje, yawan cin gyada zai iya kara ta’azzara matsalar, sakamakon maikon dake cikin gyadar. Kenan ba gyada kadai ba, duk wani abinci mai maiko zai iya ta’azzara matsalar kuraje a fuska. Don haka sai dai a rika kaffa-kaffa.

Ina da ciwon suga kusan shekaru shida kenan. Sannan ina da matsalar sha’awa, da mu’amalar iyali, shi ne nake neman mafita. Ko ana iya warkewa daga wannan matsala?

Daga A. G. Muhammad, Kaduna

Amsa: Idan kana da ciwon suga yana nufin kana karbar magungunan ciwon kenan a asibiti. Ya kamata ka zauna kai da likitan da ke ba ka wadannan magunguna wanda kuma yake bibiyar yawan sugar taka ku yi wannan magana da shi, baki da baki, domin ba magana ba ce ta jarida.

Tabbas masu ciwon suga suna daya daga cikin wadanda ke samun irin matsalar da ka zayyana saboda yawan sukarin na wa cikin jijiyoyin namiji illa. Amma akwai magungunan da za su taimaka wajen shawo kan matsalar, duka idan ka tattauna da likitan naka, ba zai ki rubuta maka wanda za ka rika amfani da su ba.

Maganar ko ana iya warkewa daga matsalar tana da girma, domin kamar ka tambaya ne ko ana iya warkewa daga ciwon sugan, wanda mu dai a likitance har yanzu ba maganin waraka sai na rage kaifin ciwon. Ana nan dai ana bincike don gano magani da zai iya warkar da matsalolin gaba daya.

Jikina yana yin wasu kuraje masu ruwa, idan suka mutu suna barin tabo. Na yi magani har na gaji shi ne nake neman shawara.

Daga B.Y da Abu Bilal

Amsa: Tun da ban ga irin kurajen ba, ba ku kuma fadi irin maganin da aka yi ba, shawara ita ce likitan fata ya duba ya gani ko kurajen mene ne. Shi ne zai ba da magungunan da idan aka yi dace aka yi amfani da su, ko kuma aka bi shawarwarin da zai ba da domin kada su dawo, to za a ci nasara.

Shin ciwon gyambon ciki yana sa amai ne? Da na fara jin murdar ciki wajen kahon zuci sai amai.

Daga Fatima A. Jakusko

Amsa: E, ciwon gyambon ciki yana sa amai, amma ba shi kadai ne ciwon ciki mai sa amai ba. Idan kika je babban asibiti aka miki aune-aune, za a iya gano ko olsar ce ko a’a.

Ni ina fama da warin baki. Na je asibitocin hakori a kasar nan wajen biyar amma ba a dace ba. Mece ce shawararka?

Daga H. J. Niger

Amsa: Ai ba ka fadi me aka maka a asibitocin hakorin ba, me kuma suka ce kana da shi. Wasu nau’ukan warin bakin fa daga cutukan ciki ne, da ma na jiki baki daya ba daga baki kadai ba. Don haka idan likitocin hakorin ba su san takamaimai inda matsalar take ba, sai ka ga likitan ciki wato bangaren internal medicine a babban asibiti.

 Wane yanayi na alamu mai hawan jini zai rika ji a jikinsa, kuma wanka da ruwa mai zafi na kawo shi?

Daga Muhammad N. Janguza

Amsa: Hawan jini ba ya kawo wasu alamu, sai dai kawai idan ya dade a jiki ba a gano shi aka fara magani ba, a ji ya fara illa a kwakwalwa, ko a zuciya, ko a koda ko a idanu. Shi ya sa ake son manyan mutane marasa matsalar su rika auna hawan jinin a kalla sau daya a shekara.

Kuma wanka da ruwan zafi ba shi ke kawo hawan jini ba, gado (wato idan akwai iyayenka da ke da ciwon), kiba, da yawan cin abu ko shan abu mai gishiri da sinadarin sodium da yawa, sune suke kawo hawan jini.

Ko akwai hanyar da mutum zai bi ya daina shan taba sigari kai tsaye?

Daga J.Y. Sokoto

Amsa: E, da yake ita sigari karama ce a kayan maye idan aka daina shanta kai tsaye ko tashi guda ba a cika samun wasu matsalolin lafiya sosai ba, sai dai ko ciwon kai da rashin sukuni, wadanda magunguna irinsu panadal za su magance. Da dama masu barin shan sigari suna dainawa ne tashi guda da kansu.

Idan mutum na so ya daina kuma yana tsoron alamun barinta zai iya neman cingam mai sinadarin da taba ke da shi, da ake kira nicotine gum, wanda za a iya samu a manyan kyamis, ya fara taunawa a kullum maimakon busa hayakin. A hankali a hankali kuma sai ya rage cin cingam din har jiki ya saba.

A likitance akwai maganin tumbi ne ko hanyar da za a bi a sace shi?

Daga Adamu S. Idris

Amsa: Akwai amma ba magani ba ne, tiyata ce. Sunanta tiyatar dame ciki, irin wadda akan wa wasu matan manyan mutane. To har maza ma ana musu, sai dai da yake mata sun fi maza tsanar tumbi, mata aka fi sani suna yi. Tiyata ce mai tsada, domin akan zuke maikon tumbin ne tas a kuma dame fatar bangon cikin, kuma da wuya a samu wadanda za su maka a wannan kasa, sai dai ko waje.

Amma idan mutum ba zai iya biya ba sai dai a ce ya rage ci, ya kuma kara zage damtse wajen yawan motsa jiki.

An auna ni an ce mini ina dauke da kwayar ciwon hanta ta Hepatitis B. Sai dai ni kalau na ke ji na, ba na ko zazzabi. To idan aka ce mutum na da kwayar cutar wata matsala ce?

Daga M. Abdullahi, Kano

Amsa: E, kwayar cutar tana illa a hanta ne dangane da karfin garkuwar jikinka, akwai wanda zai zauna da kwayar cutar har karshen rayuwarsa ba ta masa illa ba, wadanda su suka fi yawa, ba su da ko alamar wani ciwo. Akwai kuma wadanda take wa hantarsu illa a sannu a sannu, akwai kuma wadanda tashi guda take kashe mu su hanta. Da yake har yanzu ba maganin kashe kwayar cutar a likitance, sai dai kawai a zuba mata ido a gani, a yi ta addu’a, ana hoton scanning na hanta duk shekara. Amma idan ta fara taba hanta za a fara jin alamu, ya nuna kuma a hoton, kuma a wannan lokaci sai an nemi magungunan rage kaifin kwayar cutar, wadanda ke da matukar tsada sosai.

Akan kuma ba masu ita shawara kada su auri wadda bata da kwayar cutar don kada a yada ciwon.