✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi da suka shafi ciwon kai

Mene ne ke kawo ciwon kai na bari daya? Daga Aminu Adam Mallam-Madori Amsa: Akwai ciwon kai nau’i-nau’i; wasu gadonsu ake yi, wasu ciwon wasu…

Mene ne ke kawo ciwon kai na bari daya?

Daga Aminu Adam Mallam-Madori

Amsa: Akwai ciwon kai nau’i-nau’i; wasu gadonsu ake yi, wasu ciwon wasu sassan jiki ke kawo su, wasu kuma ciye-ciye da shaye-shaye da yawan aiki da gajiyar yau da kullum ce ke kawo su. Shi ciwon kai na bari daya da muke kira migraine ana ganin kamar yana cikin wadanda akan gada a tsatso, kuma mata sun fi maza yinsa. Don haka idan mutum na da ciwon ba a sa ran zai rabu da shi gaba daya, kamar dai farfadiya ko ciwon suga ko na hawan jini, sai dai ya zo ya tafi, ya zo ya tafi. Don haka mai irin wannan sai dai ya rika zuwa kamar wurin likitan kwakwalwa ana rubuta masa magunguna masu karfi da za su rika kiyaye tashin ciwon da kuma magance shi idan ya tashi din, domin magunguna kanana irinsu panadal ba sa masa.

 

Ni na sha sigari a da, to amma yanzu na daina. To sai nake jin yawan ciwon kai. Ko hakan na da alaka da barin sigarin?

Daga Muhammad H. Tsagero

 

Amsa: E, ba mamaki dalilin barin sigarin ne ke jawo maka ciwon kai. Da yake ka san shi sinadarin nicotine na sigarin kwakwalwa yake cazawa, to rashinsa zai iya sa kwakwalwar begensa, ta hanyar ciwon kai. Dama ai ba kowa ne zai iya barin sigari haka nan kawai ba tare da taimakon likitan kwakwalwa ba. Wasu sukan iya jure wa ciwon kan da kan biyo baya, wasu kuma ba sa iyawa. Idan kwayoyin rage radadin ciwon kai kamar panadal ba sa maka akwai magungunan da za a iya ba ka domin rage wannan ciwon kai idan ka ga likitan kwakwalwa. Wasunsu nau’in cingam, wasu nau’in kwaya wasunsu kuma na’in maganin likawa a fata.

 

Ni ma ina fama da azababben ciwon kai, ga bacin rai da damuwa da yawan tunane-tunane. 

Daga M.A., kwalli

Amsa: Kai ma kana bukatar ganin likitan kwakwalwa Malam kwalli.

Ni kuma zafin kirji da bugun zuciya da sauri da yawan tsoro. Na wa mahaifiyata magana ina so in je asibiti ta ce damuwa ce kawai ba sai na je ba. Shine nake neman shawara.

 

Amsa: A’a ai ba za a kira irin wadannan alamomi da cewa damuwa ce kawai ba. Zafin kirji da bugun zuciya da sauri na nufin sai an duba zuciyarka an maka hotuna da aune-aunen jini an tantance ko mene ne. Tabbas kana bukatar ganin likita kaima. Idan ka sayi wannan mujalla ka nuna mata wannan shawara da aka ba ka cewa damuwa ba kawai ba ce. Idan ba a yi magani tun yanzu ba, za ta iya jawo maka ciwon da zai wahalar magancewa nan gaba idan ma ba a riga aka makara ba.

 

Muna so ka fadakar da mu a kan shan shisha domin wasu ba su sani ba.

Daga Mannir Abbatuwa, Kano

 

Amsa: Ai wannan ma mun fadi hadarinta a rubutun baya. Idan wasu mutane ba su sani ba ka ce musu illarta ta ninka ta sigari kusan sau dari saboda ita zuka daya tamkar shan kara dari ce. Wato duk sha daya hadarin cikin sugari sau dari ko ma fiye mutum zai samu.

 

Wai ciwon suga yana da magani kuwa?

Daga Mallam Musa, Potiskum da Aisha, Katsina

 

Amsa: A likitance sai dai maganin kwantar da sukarin babu na waraka har yanzu. Muna sa rai watakila dai nan gaba.

 

Yaya ake shan magungunan tsutsar ciki irinsu mebendazole da albendazole da aka taba bayani? Kuma zan iya sha don riga-kafi?

Daga Idi, Maiduguri

 

Amsa: Dama ai don riga-kafin muka fi ba da karfin cewa za a iya sha a kalla sau daya a shekara, a yara kuma a kalla sau biyu a shekara duk bayan watanni shida. A wurin da ka sayi maganin za ka tambayi yadda ake amfani da shi, tunda yawanci masu kyamis suna aje kwararrun masana magunguna wato Pharmacist.

 

Wai da gaske ne naman ganda ba ya da wani amfani?

Daga Nasiru Shehu Sokoto

 

Amsa: Haka dai masana cimaka suka ce, cewa wai duk kitse ne babu wata mamora. Don haka sai a yi taka-tsantsan da shi.

Me ke kawo maiko a fuska mai fari-fari kamar tsiro? Kuma ya fi fitowa a kan hanci. Mene ne maganinsa?

Daga Maryam, Birnin Kudu

Amsa: Maikon da muke ci a abinci ai dama ba shi da wurin taruwa sai karkashin fata da jikin magudanan jini. Idan mutum na son ya yi maganin maiko sai ya rage cinsa.

 

Ni ina yawan yin ciwon typhoid, ko me ya sa hakan?

Daga Ummi S.

 

Amsa: Ciwon typhoid in dai an aunaki an tabbatar shi ne kazantar abinci da abin sha ne ke kawo su. Idan mutum ya kasa rabuwa da ciwon yana nufin abincinsa da abin shansa ba tsabtatattu ba ne. Ki binciki rubuce-rubucen wannan shafi na can baya za ki ga hanyoyin kariya daga ciwon typhoid.

 

Wani lokaci idan na ci abinci na koshi sosai sai na ji numfashina kamar zai dauke, ga motsi a ciki ga tashin zuciya kamar na yi amai. Me ke kawo hakan?

Daga Muhammad Sulaiman DBR

 

Amsa: Abubuwa da dama za su iya kawo maka haka, tun daga cin zari, zuwa tsutsar ciki zuwa ciwon typhoid ko shigar sauran kwayoyin cuta ciki. Don haka zama bai ganka ba, kana bukatar ganin likita da aune-aune da gwaje-gwajen jini da fitsari da ma na bayan-gida watakila a ga ko za a ga kwayayen macijin ciki. Amma dai kafin ka je za ka iya fara jarraba rage sanwa tunda ka ce kana ci kana take ciki. Shima wannan zai iya sa tashin numfashi sama-sama da jin kamar za a yi amai.