✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aminiya: Yaushe kuka kafa wannan kungiyar?

Alhaji Mainasara Moussa shi ne shugaban kungiyar ‘yan Nijar mazauna Bauchi cikin tattaunawarsu da wakilinmu, ya yi tsokaci game zamantakewar  ‘yan Nijar a jihar  da…

Alhaji Mainasara Moussa shi ne shugaban kungiyar ‘yan Nijar mazauna Bauchi cikin tattaunawarsu da wakilinmu, ya yi tsokaci game zamantakewar  ‘yan Nijar a jihar  da sauran batutuwa.  Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Farko za mu so ka fara gabatar da kanka?

Alhaji Mainarasa Moussa: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukacin sarki. Sunana Alhaji Mainarasa Moussa shugaban kungiyar ‘yan Nijar mazauna Bauchi na yi matukar farin ciki bisa wannan dama domin yin tsokaci game da halin da ‘yan Nijar suke ciki a Jihar Bauchi.
Aminiya: Yaushe kuka kafa wannan kungiyar?
Alhaji Mainarasa Moussa: Mun kafa wannan kungiya ne sama da shekara 20 da suka gabata. Kuma a lokacin mulkin gwamnan Jihar Bauchi marigayi Tatari Ali kuma Alhaji Hamma shi ne shugaban kungiyar na farko, sai kuma Alhaji Ali Mai kilishi bakin.
Kafin na zama shugaban kungiyar ni ne sakataren kudi na kungiyar sannan na rike mukamin mataimakin shugaban kungiyar na kusan shekara 12. Yau shekara daya ke nan ina rike da mukamin shugaban kungiyar na jiha.
Aminiya: Mambobin wannan kungiya sun kai mutum nawa a jihar Bauchi?
Alhaji Mainarasa Moussa: Muna da mambobi wadanda muka musu rijista a kungiyar sama da mutum dari tara 900, sai dai kuma kasan akwai wadanda suke zaune ba tare da rijista a kungiyar ba don haka muke ba da shawara ga duk wani dan Nijar da ya zo ya yi rijista damu domin ta haka ne zamu ga ne daga wata jiha ya fito a Jamhuriyar Nijar.
Kuma jihohi 36 har da Abuja dukka akwai shugabannin gudanarwa na ‘yan Nijar mazauna Najeriya. Muna yin taro a duk karshen shekara sannan muna da shugaba na kasa baki daya kamar yadda ko wacce jiha take da shugaba.
Aminiya: Wasu irin sana’o’i mambobin kungiyarku suke yi a jihar Bauchi?
Alhaji Mainarasa Moussa: Kadan daga cikin abubuwan da mambobin wannan kungiya suke yi akwai masu sayar da tsire akwai masu sayar da shayi akwai masu sayar da taba sigari akwai masu sayar da burodi da sauran kananan sana’oi wanda mutum zai samu abin da zai ciyar da iyalansa kuma mambobinmu muna bamu dukkan goyon bayan da ya kamata.
Aminiya: Idan mutum yazo yana so a masa rijista wasu hanyoyi zai bi?
Alhaji Mainarasa Moussa: Na farko bama rijista wa mutum sai ya zo mana da takardan shaida na hukumomin tsaro bayan haka sai ya nuna mana daga wace jiha ya fito a Jamhuriyar Nijar. Kuma wani sana’a yake yi a Bauchi wadannan su ne kadan daga cikin dokokin shiga kungiyar.
Aminiya: Shekararka nawa a Jihar Bauchi?
Na shafe sama da shekara 20 ina zaune a cikin garin Bauchi kuma ina zaune da al’umma lafiya. Ina da mata biyu da yara 11 masu rai a duniya.
Aminiya:Wasu matsaloli ‘yan Nijar mazauna Bauchi suke fuskanta a halin yanzu?
Alhaji Mainarasa Moussa: A gaskiya babu wani matsala da ‘yan Nijar mazauna Bauchi suke fuskanta a halin yanzu domin muna da alaka mai kyau tsakaninmu da hukumomin tsaro da sarakunan gargaji da sauran masu ruwa da tsaki a jihar saboda haka muna fatar alheri ga kowa da kowa.
Ina kuma godiya ga dimbin mambobin wannan kungiya bisa yadda suke bin doka da oda wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum duk mutanen da suke bin doka to tabbas zaka ga rayuwarsu ta yi daban da sauran masu karya doka.
Aminiya: Wane lokaci kuke yin taron kungiyarku?
Alhaji Mainarasa Moussa: Muna zama domin tattauna matsalolin kungiya a duk karshen wata.Kuma muna tara kudi domin tallafawa wadanda suke cikin mawuyacin hali ko ‘yan gudun hijira da suka fito daga jihohin da ake fama da tashe-tashen hankula na ‘yan kungiyar Boko Haram.
Aminiya: Me ye sakonka ga ‘yan Nijar mazauna Bauchi?
Alhaji Mainarasa Moussa: Babban sakona ga ‘yan Nijar mazauna Bauchi shi ne su rika bin dokokin Najeriya sannan suyi hakuri da abin da suke samu. Ba a gaggawa a rayuwa duk wanda ya yi hakuri da kadan, sai Allah Ya rufa masa asiri duniya da lahira. Kada a manta un kafa wannan kungiya ne domin bunkasa rayuwar ‘yan Nijar.
Kuma wannan kungiya za mu ci gaba dayin addu’oi na musamman ga gwamnatin Najeriya Allah Ya kawo mana karshen matsalar tsaro da ya addabi yankin Afirka dama duniya baki daya.
Idan Najeriya ta zauna lafiya dukkan kasashen Afirka za su samu zaman lafiya da bunkasar tattalin arzikin kasa kuma da Najeriya da Nijar kamar dan juma ne da dan jummai.
Aminiya: wane kira kake da shi ga sabon shugaban Najeriya?
Alhaji Mainarasa Moussa: Abin da muke fatar sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ga ’yan Nijar mazauna Najeriya shi ne ya magance matsalar tsaro wadda ya gurgunta yankin Arewa-maso-Gabas. Bayan haka, muna fatar zai farfado da kananan masana’antun da suka kwanta dama shekara da shekaru. Idan ya yi haka cikin kankanin lokaci talauci zai zamo sai tarihi a daukacin kasar nan baki daya.
Har ila yau, babban sakona ga daukacin ‘yan Nijar mazauna Najeriya shi ne ayi hakuri da juna babu al’ummar da za ta samu ci gaba, sai da zaman lafiya da hadin kai.